Mafarin rayuwar dan Adam a Afirka | Tushen Afirka: mutanen da suka taka rawa a tarihin Afirka | DW | 23.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Tushen Afirka

Mafarin rayuwar dan Adam a Afirka

Kwarangwal Lucy wacce aka fi sani da suna Dinknesh tana da shekaru miliyan 3.5. Kuma kasusuwa ne na bil Adama. An ganota a shekara ta 1974 a kasar Habasha.

Lucy ita ce kwarangwal mafi dadewa kana cikakka na halittan dan adam na farko da ba a taba samun irinta ba a karni na baya bayanan Lucy ta taimaka wajen sanin ci gaban tushen bil adama.

A shekarun 1974 masu binciken kimiyya suka samu kasusuwan dake da kama da na mutum cikin jejin Rift na kasar Habasha. Cikin murnan masanan da kwararru suna yin biki murna suna saurarn wani kida na Lucy in the sky wanda makinda Beatles suka raira wannan waka, sannan daga nan ne kuma kwarangwal din ta dauki wannan suna na Lucy. Bayan makonni biyu na bincike cikin zafin rana tawagar masu bincike sun tono daruruwan kasusuwan Lucy, wacce ta zama kwarangwal mafi zama cikakka ta bil dama na farko wanda ba a taba samun irinta ba kamar yadda wani masain tarihi na halitu da tsirai Berhane Asfaw ya bayyana.

''Kashi 40 cikin dari na jikin Lucy yana yadda yake, za a iya gane ta bambanta da sauran halittu na wancan zamani. Lucy ta zama wata hanyar bincike ta farko ta yin nazarin ci gaban halitar dan Adam shekaru da dama.''

A dubi bidiyo 01:20
Now live
mintuna 01:20

Dan Adam ya fara rayuwa a Afirka

Lamarin yana da daukar hankali game da irin yadda samun wadannan kayan tarihi shi ne irinsa mafi dadewa da aka samu, masana sun saukaka abin ta yadda za a iya fahimtar tushe da ci gaban halittar dan adam a cewar dokto Robert Blumen Schine jagoran cibiyar binciken halittu da tsirai na Afirka ta Kudu.

''A zahiri wata halitta ce da abin da ya yi mata saura su ne kai da hakora wadan da ke da mahimmanci a cikin aikin bincike don gane nau'in abinci da take ci da kuma girman kwakwarta, amma kuma da wasu sauran kasusuwan da ke nuna cewar tana tafiya ne bisa kafafunta.''

Lucy ta kan iya tafiya kamar dan adam sai dai kuma tana wasu irin alamonin iri daya da na biri, hannayenta sun lankwasu kuma sun fi kafafunta tsawo abin da ya sa ake tunanin ta kwashe rayuwarta a hawan bishiya, tsawonta ya kai sama da mita daya. Gano wannan karangwal na Lucy tare da wasu kasusuwan, ya nuna cewa Afrika ne cibiyar bil Adama a cewar dokrto Robert Blumenschine

"Duk alamonin gwangwan birin da ake iya kamantasu da bil adama sun bayyana ne a nahiyar Afirka, daga kwakwarya da tunani na dan adam wasu abubuwa ne da suka banbanta sai dai kuma wani ci gaban halitta hasalima a Afirka.''

'Yan Habasha da dama sun fi son su kira Lucy da sunan Dinknesh abinda ake nufi da abin mammaki. Saboda Lucy ita kadai take ana kuma ajiye da ita ne a gidan ajiye kayan trihi na kasar. Ba a fitar da ita sai akwai wani babban taron baje koli na musammun, sai dai a kan samu kwarangwal na platre da ake yi wasu sasan duniya tamkar Lucy wanda ake ajiye da su a gidajen tarhi har ma ta intanet akan iya samunsu.

Sauti da bidiyo akan labarin