Madugun yan tawayen kongo ya yi kiran tsagaita wuta | Labarai | DW | 11.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Madugun yan tawayen kongo ya yi kiran tsagaita wuta

Madugun yan tawayen ƙasar Congo janar Laurent Nkunda ya yi kiran tsagaita wuta bayan sake ɓarkewar faɗa wanda ya jawo hasarar mayaƙan tawaye su 85. A can baya Nkunda ya sa kafa ya shure yarjejeniyar da aka cimma bisa shiga tsakani na Majalisar ɗinkin duniya. Dauki ba dadin na baya bayan nan ya auku ne a lardin arewacin kivu. Laurent Nkunda wanda yace yana yaƙi ne domin kare yan ƙabilar Tutsi marasa rinjaye, yace yanzu a shirye yake domin shawarta shigar da mayaƙan sa cikin rundunar sojin ƙasa kamar yadda gwamnati kongo da kuma majalisar ɗinkin duniya suka buƙata.