1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Macron ya bukaci sake fasalin EU

Gazali Abdou Tasawa
April 17, 2018

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana bukatar sake fasalin Kungiyar Tarayyara Turai da sake gina demokardiyya a cikin kasashen nahiyar Turai domin tunkarara kalubalan rarrabuwar kawuna a Turai.

https://p.dw.com/p/2wCGG
Frankreich Rede Macron vor dem Europaparlament
Hoto: Reuters/V. Kessler

Daga cikin bukatun da shugaban kasar ta Faransa ya nema har da sake fasalin Kungiyar Tarayyara Turai da sake gina demokardiyya a cikin kasashen nahiyar Turai domin tunkarara kalubalan rarrabuwar kawuna da ake fuskanta a tsakanin kasashen nahiyar Turai da kuma musamman komabayan demokradiyya inda jam'iyyun masu kyamar baki ke kara samun gindin zama da ma karbe iko a wasu kasashen nahiyar.

Shugaba Macron ya gabatar da wannan shawara tasa ce a jawabin da ya gabatar a wannan Talata a zauran majalisar dokokin Tarayyar Turai a birnin Strasbourg inda ya ce lokaci ya yi na kasashen Turan su kauce wa sake irin kuskuren da suka yi a baya , na kin maiyar da hanhali ga hadin kan Turai da komawa zarge-zargin juna wanda ya ce na barazana ga makomar nahiyar da kungiyar ta EU.

Kazalika Shugaba Macron ya ce Faransa a shirye Faransa take ta kara yawan kason kudadenta a cikin kasafin kudin Turai na bay daya da Kungiyar ta EU ke son girkawa bayan kammala aiwatar da shirin ficewar Birtaniya daga cikin Kungiyar ta EU. 


Bugu da kari Shugaba Macron ya kuma bayar da shawarar girka wani asusu na musamman a tsakanin kasashen Turai wanda zai samar da kudaden tallafa wa kananan hukumomi na kasashen Turai da ke karbar 'yan gudun hijira a wani mataki na kawo karshen muhawarar da ta ki ci ta ki cinyewa tsakanin kasashen na Turai kan batun kasafa 'yan gudun hijira a tsakanin kasashen Kungiyar EU.