Macin ƙin jinin gwamnatin sojin Myanmar na kara yin tsamari
September 24, 2007Gwamnatin tarayyar Jamus ta yi maraba da zanga-zangar lumana na kin jini gwamnatin mulkin sojin kasar Birma. Wani kakakin ma´aikatar harkokin waje ya nunar da cewa a kullum ministan harkokin wajen Jamus F.-W. Steinmeier na goyon baya aiwatar da canje canje a Birma tare da yin wata tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin mulkin soji da masu neman sauyi. A yau ma dai dubun dubatan sufaye da fararen hula sun ci-gaba da macin kyamar gwamnati a babban birnin kasar Rangoon, kwana na 7 a jere. Kawo yanzu zanga-zangar na tafiya cikin lumana amma ana kara nuna fargabar cewa dakarun tsaro ka iya murkushe ta. Soe Aung na wata kungiyar ´yan majalisar dokokin Burma wanda ke gudun hijira a Thailand ya ce al´umar kasar na kara samun karfin guiwar nuna adawa da gwamnati.
Soe Aung:
“Ya zama wajibi gwamnatin mulkin sojin ta san cewa ba zata ci-gaba da mulki har abada ba. Dole ne ta sasanta da jama´a dole ne kuma ta sasanta da sauran shugabannin siyasa.”