1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a hadarin jirgin kasa a Indiya

November 20, 2016

Jirkicewar taragu 14 ta haddasa mummunan hadarin jirgin kasa da ya lamshe rayukan mutane da dama a arewacin Indiya. Ba a san musabbabin hadarin ba tukuna.

https://p.dw.com/p/2Sxf0
Expresszug entgleist: Viele Tote bei Zugunglück in Indien
Hoto: Reuters/ANI

Akalla mutane 91 sun rasa rayukansu yayin da wasu karin 150 suka jikata a wani hadarin jirgin kasa da ya auku da sanyin safiyar wannan lahadin a arewacin kasar Indiya. Taragu 14 ne suka jirkice lokacin da jirgin ya kauce hanya bayan da ya taso daga garin Indore i zuwa Patna.

Kawo hanzu dai ba a bayyana sanadin hadarin jirgin ba, amma dai ya na zama na biyu mafi muni tun bayan faduwar jirgin kasa ta 1981 wacce ta yi sanadin mutuwar mutane 800 a Indiya. Tuni dai hukumomin kasar suka sanyan asibotin yankin Arewacin Indiya a cikin shirin ko ta kwana da nufin kula da wadanda hadarin ya ritsa da su.

Speto janar na 'yan sanda Zaki Ahmad ya ce aikin ceto na ci gaba da gudana. Mun tsamo gawarwakin mutane kimanin 63. Biyu daga cikin taragun sunyi matikar lallace sosai. Mun yi amfani da kayayyakin gargajiya wajen tsamo wadanda suka sami rauni."