1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mace-mace a hadarin jirgi kasa a Bulgeriya

JIrgin da ke dakon isakar gaz ya kauce hanya a lokacin da yake ratsa wani kauye na yankin Arewma maso gabashin Bulgeriya, lamarin da ya haddasa mutuwar mutane biyar.

Akalla mutane biyar sun mutu sakamakon tarwatsewar wani jirgin kasa mai dauke da tankunan iskar gaz a Bulgeriya, bayan da ya saki hanyarsa tare da ragargajewa a tsakiyar wani kauye da ke Arewa maso gabashin kasar. Sai dai hukumomin yankin sun ce adadin dai na iya karuwa ganin yadda hadarin ya yi muni sosai.

Faduwar jigin kasan mai cike da ban mamaki, ta kuma haddasa jin ciwon mutane da dama tare da latata tashar jirgin da dakunan ma'aikatan gami da wasu gidaje fiye da 20 a yankin Hintrino. Hukumomin sun yi kokarin kwashe mutanen baki dayansu bisa dalillai na tsaro, yayin da masu ayyukan ceto ke ci gaba da bincika baraguzzan gidajen da suka ruguje.

Ministan kiwon lafiyar kasar ta Bulgeriya Petar Moskov ya ce akalla mutane 29 ne aka kwantar a asibiti sakamakon konkonewar da suka yi.