1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace-mace a hadarin jirgin sama a Kaduna

Ibrahima Yakubu/AHAugust 29, 2015

Aƙalla mutane bakwai sun rasa rayukansu bayan da wani ƙaramin jirgin sama ya yi haɗari a Kaduna da ke Arewacin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1GNpG
Nigeria Lagos Flugzeugabsturz
Hoto: picture alliance/AP Images

Da misali karfe bakwai na safiyar Asabar ne jirgin saman kirar Donnier Aircraft ya yi haɗari a kusa da cibiyar horas da sojojin Najeriya na NDA da ke Kaduna. Ba a dai bayyana musabbabin faɗuwar jirgin ba, amma dai na horas da sojoji dabarun tuki ne.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA da sauran ƙungiyoyin agaji sun kai ɗauki don ceto rayukan waɗanda suke cikin jirgin. Sai dai kuma Umar Abdullahi na kungiyar Red Cross ya bayyana cewar ba wanda aka ciroshi da rai.