Mabiya addinin kirista na gudanar da bukukuwan sallar kirsimeti | Labarai | DW | 25.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mabiya addinin kirista na gudanar da bukukuwan sallar kirsimeti

Shugaban darikar katolika na duniya, wato Fafaroma Benedict na 16 ya bukaci kasashen duniya, dasu martaba tare da kare mutuncin yara.

A cikin wani jawabi daya gabatar a gaban dubbannin mabiya darikar katolika a daren jiya, wayewar garin yau, fafaroma ya mayar da hankali ne ga kana nan yara da ake tursasa musu aikin soji da kuma wadanda ke cikin kangi na talauci.

Bugu da kari shugaban darikar ta katolika ya kuma janyo hankalin mabiya addinin kirista dasu daina bawa harkokin kyale kyale fifiko a lokacin sallar kirsimeti.

A nan gaba kadan ne a yau ake sa ran Fafaroma Benedict na 16, zai gabatar da jawabin sa na biyu bisa al´ada, game da wannan muhimmiyar rana ta kirsimeti