1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

M.Abbas ya rusa gwamnatin haɗin kan Palestinu, tare da kafa dokar ta ɓace

A ɗazunan Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya sa hannu a kann dokar rusa gwamnatin haɗin kann ƙasa, tare da dokar ta ɓace a fadin ƙasar baki ɗaya.

Kazalika shugaban hukumar Palestinawa ya ambata shirya saban zaɓe, da zaran al´ammura sun daidaita.

Mahamud Abbas ya dauki wannan mataki, a matsayin martani ga tashe-tashen hankullan da ke wakana tsakanin ƙungyiyoyin Fatah da na Hamas.

A yammacin yau dakarun Hamas, sun bayyana fille kann wani jigo a ƙungiyar fatah, kazalika sun yi kaca-kaca, da gidan rediwan muryar Palestinu.

Rikici tsakanin ɓangarorin 2 a yau alhamis ya hadasa mutuwar mutane kimanin 20.

A halin da ke ciki, ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban na dunia, na ci gaba da yin Allah wadai da wannan tashe-tashen hankulla.

Masu kulla da harakokin da ke gudana a gabas ta tsakiya, sun danganta rusa gwamnatin Palestinu, a matsayin da zai ida dagula zaman lahia a wannan yanki.