M.Abbas ya rusa gwamnatin haɗin kan Palestinu, tare da kafa dokar ta ɓace
June 14, 2007A ɗazunan Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya sa hannu a kann dokar rusa gwamnatin haɗin kann ƙasa, tare da dokar ta ɓace a fadin ƙasar baki ɗaya.
Kazalika shugaban hukumar Palestinawa ya ambata shirya saban zaɓe, da zaran al´ammura sun daidaita.
Mahamud Abbas ya dauki wannan mataki, a matsayin martani ga tashe-tashen hankullan da ke wakana tsakanin ƙungyiyoyin Fatah da na Hamas.
A yammacin yau dakarun Hamas, sun bayyana fille kann wani jigo a ƙungiyar fatah, kazalika sun yi kaca-kaca, da gidan rediwan muryar Palestinu.
Rikici tsakanin ɓangarorin 2 a yau alhamis ya hadasa mutuwar mutane kimanin 20.
A halin da ke ciki, ƙasashe da ƙungiyoyi daban-daban na dunia, na ci gaba da yin Allah wadai da wannan tashe-tashen hankulla.
Masu kulla da harakokin da ke gudana a gabas ta tsakiya, sun danganta rusa gwamnatin Palestinu, a matsayin da zai ida dagula zaman lahia a wannan yanki.