Ma´anar Visa Schengen | Amsoshin takardunku | DW | 23.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Ma´anar Visa Schengen

Ƙasashen da ke amfani da Visa Schengen. Manufar Visa Schengen da bambancinsa da sauran Visa ?

default

Visa Schengen

Schengen wani ɗan ƙaramin gari ne da ke ƙasar Luxemburg, gap ga iyaka tsakanin Luxemburg, Faransa da Jamus.

Kuma dalilin da ya sa a ke cewa Visa Schengen saboda a wannan gari ne wasu ƙasashen Turai guda biyar wato Jamus,Faransa Beljiam, Holland, da Luxemburg ranar 14 ga Juni na shekara 1985 su ka rataba hannu kan yarjejeniya da ta samar da Visa na bai ɗaya.

 Babbar manufar Visa Schengen itace, sauƙaƙa zirga zirga tsakanin al´ummomin wannan ƙasashe.

Misali kamin wannan yarjejeniya mutumen da ke Jamus ya na buƙatar zuwa Luxemburg ,sai ya nemi Visa ga ofishin jikadancin Luxemburg da ke nan Jamus, idan ya na buƙatar zuwa Faransa, sai ya samu Visa daga ofishin jikadancin Faransa, haka duk sauran ƙasashen.Amma da aka samu Visa Schengen ya wadatas,idan mutum na da shi, zai bashi damar ya shiga duk sauran ƙasashen da su ka rattaba hannu akan wannan yarjejeniya.

Da farko su biyar ne, amma a hankali a hankali sauran ƙasashen turai su ka ga fa´idar wannan Visa, sai suma su ka buƙaci shiga ciki.

Daga biyar sai su ka koma ƙasashe 15, wato kenan a ka samu ƙarin ƙasashe goma sune: Sweeden,Portugal, Nowe, Italiya, Island Girka, Finlande, Spain, Danmark da Austriya, idan ka haɗa da ƙasashe biyar na farko ,wato Jamus, Faransa, Luxemburg Holland da Beljiam 15 kenan.

A shekara ta 2008 an samu ƙarin ƙasashen Turai  goma, wanda suma su ka shiga rukunin ƙasashe masu amfani da wannan Visa ta bai ɗaya, wato Visa Schengen wannan ƙasashe kuwa sune: Malta, Estoniya Latbiya,Lithuaniya, Hongrie,Poland, Jamhuriya Cek,Slovakiya, Sloveniya, da Swizland.

A jimilce ƙasashe 25 kenan,saboda haka,da visar ƙasa ɗaya memba, mai Visa Schengen zai iya shiga duk wannan ƙasashe 25.

A yanzu haka kuma ƙasashen Lieschtenstein, da Vatikan sun shiga tattanawa da zuma zama membobi cikin rukunin ƙasashe masu amfani Visa Schengen.

Idan ka na da Visa Schengen daga Jamus, za ka iya shiga ko wace ƙasa daga wannan ƙasahe 25 da na zana maka, za ka iya zama ciki, har tsawan watani ukku cikin watanni shidda, kenan a shekara za ka iya zama na tsawan watani shida.

Akwai ƙasashe biyar membobin EU,wanda batun  Visa Schengen ba  shafe su ba wannan ƙasashe su ne:Ingila,Irland,Bulgariya,Rumaniya da Syprus.Ko ka na da Visa Schengen, idan za ka tafi bulaguro wannan ƙasashe sai ka tambayi Visa.

Sannan kuma a ɗaya hannun, ba duka ƙasashen Schengen ba, ke membobin a EU, misali Swizland, Island da Nowe ai ka ga su na cikin Visa Schengen, amma ba su cikin rukunin ƙasashe membobin Ƙungiyar Tarayya Turai.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmed Tijani Lawal