Ma´amila tsakanin Jamus da Rasha
October 13, 2010Talla
Sugaban ƙasar Jamus Christian Wulff, na ci gaba da ziyara aikin kwanaki huɗu da ya kai a Rasha.A yau ya gana da takwaransa Dmitri Medvedev a birnin Mosko, inda su ka tattana kan batutuwa dabamdaban da su ka jiɓanci hulɗoɗi tsakanin ƙasashen biyu.Wulff ya buƙaci game ƙarfi da Rasha wajen yaƙi da ta´adanci da kuma ɗumamar yanayi.
A ɗaya wajen sugaban ƙasar Jamus ya yi kira ga humomin Kremlin su ƙara himmantuwa wajen kare haƙƙoƙin bani Adama.
Nan gaba a yau shugaba Christian Wullf zai gana da Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani Adama na ƙasar Rasha.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu