1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barack Obama ya kai rangadin farko a Asiya.

November 12, 2009

Shugaban ƙasar Amurika Barack Obama ya kai riyara farko a Asiya da zumar ƙarfafa hulɗoɗi.

https://p.dw.com/p/KUgJ
Ziyarar Barack Obama ta farko a AsiyaHoto: AP

A wannan alhamis ɗin ne shugaban ƙasar Amurika Barack Obama ya fara rangadinsa na farko a yankin Asiya, inda ɗaya bayan ɗaya zai ziyarci ƙasashen Japan, Singapour, China, da Korea ta Kudu.

Ma´amala tsakanin Amurika da yankin Asiya na dogon tarihi, saidai a halin da ake ciki ta na fuskantar wani yanayi na koma baya dalili da ƙarfin fada aji da ƙasar Sin ke samu a yankin.

Shugaba Barack Obama zai amfani da wannan dama domin zafafa wannan hulɗoɗi kamar yadda Ben Rhodes wani mai bashi shawara ya nunar: Ɗaya daga cikin mahimman saƙwannin da shugaban zai isar da su shine cewar, Amurika na da muradin ƙarfafa hulɗoɗi tsakanin ta da Asiya ta fannoni dabam dabam a wanan ƙarni na 21.

A matakin farko na wannan rangadi, Obama zai yada zango a birnin Tokiyo na ƙasar Japan inda zai gana da Firaminista Yukio Hatoyama, dontattana batutuwa dabamdabam da suka jiɓanci hulɗoɗi tsakanin ƙasashen biyu.

Daga nan sai ya zarce Singapour kamin ya isa biranen Shangai da Pekin na ƙasar Sin.

Zai kammalla wannan rangadi da Korea ta Kudu ranar 18 ga watan da muke ciki.

A cewar Jeffry Bader wani ba´amirike kuma masani akan harakokin tsaro a gabacin Asiya, jama´ar yankin na shawar hulɗa da Amurika amma fa da sharaɗi:Al´umomin yankin na lale marhabin da hulɗoɗi tare da Amurika, to saidai suna buƙatar gudanar da wannan hulɗa kafaɗa da kafaɗa ba hulɗa ba irin ta kashin dankali, inda manya ke taushe ƙanana, sannan suna buƙatar Amurika ta janye sojojinta daga yankin, saboda haka ne ma muka kwashe wasu dakaru daga Japan da Korea ta Kudu."

A cikin wannan ziyara babu shakka shugaba Barack Obama zai maida hankali matuƙa a game da harakokin siyasa da diplomatiya to saidai batun tattalin arziki na daga cikin mahimman batutuwan da zai tattana da magabatan ƙasashe,bugu da ƙari zai masanyar ra´ayoyi da hukumar APEC, wadda ke kula da cigaban tattatalin arzikin ƙasashen Asiya da na Pacific, kamar yadda mai bashi shawara ta fannin harakokin tattalin arziki Michael Froman yayi bayani: Shugaban na buƙatar ganin shigi da ficin hajojin ya bunƙasa ya na da burin haɓɓaka cinikayya ta yadda ɓangarorin biyu zasu ci moriya tare da ƙara buda kofofin kasuwaninsu da kuma samar da ƙarin yawan aiki ga marasa aiki.

Tare da magabatan China, bayan ma´amalar saye da yasarawa, shugaba Barack Obama, zai taɓo batun matsalar ɗumamar yanayi, da tashe tashenhankula a ƙasashen Afganistan da Pakistan, da kuma rikicin nukleyar Iran da Korea ta Arewa.

Mawallafi:Christina/ Yahouza

Edita: Aliyu