Maaikatn mai a najeriya sun janye yajin aiki | Labarai | DW | 14.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Maaikatn mai a najeriya sun janye yajin aiki

Kungiyoyin maaikatan mai a Najeriya da suka shiga yajin aiki a jiya sun sanar da dakatar da yajin aikin kwana guda bayan sun kaddamar da shi.

Kungiyoyin na kanana da manyan maaikatan wato NUPENG da PENGASSAN tun farko sunyi kira ga yajin aiki na kwanaki 3 daga jiya laraba,domin nuna bacin ransu dangane da tashe tashen hankula a yankin naija delta,dake da albarkatun mai a taraiyar najeriya.

Shugaban kungiyar PENGASSAN Peter Esele yace sun janye yajin aikin ba tare da bata lokaci ba,kuma yace yana sa ran mafi yawan membobinsu zasu koma bakin aiki a gobe jumaa idan Allah ya kai mu.