1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma’aikatar tsaron Amirka ta umarci sojojin ƙasar da su kiyaye ƙa’idojin yarjejeniyar Geneva.

September 7, 2006
https://p.dw.com/p/BukS

Ma’aikatar tsaron Amirka, wadda aka fi sani da sunan Pentagon, ta ba da wata sabuwar sanarwa inda ta umarci duk sojojin ƙasar da su dinga kiyaye ƙa’idojin yarjejeniyar Geneva, wadda ta haramta gallaza wa fursunoni. Wannan umarni dai ya shafi duk waɗanda sojojin ke tsare da su ne, ba tare ma da yin la’akari da matsayinsu a huskar shari’a ba.

Masharhanta dai na ganin wannan manufar, wato mai da hannun agogo baya ne da gwamnatin shugaba Bush ta yi. Da can dai mahukuntan birnin Washington sun ce yarjejeniyar ta Geneva ba ta shafi mayaƙan ƙungiyar Taliban, ko na al-Qaeda ko kuma na wasu ƙungiyoyin ’yan ta’adda ba. Sabon umarnin da ma’aikatar tsaron ta bayar, ya haramta duk wata gallaza wa fursunoni da dakarun Amirkan ke yi, musamman a lokacin yi musu tambayoyi.