Ma´aikatan sufuri a New-York sun amince da komawa bakin aiki | Labarai | DW | 22.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma´aikatan sufuri a New-York sun amince da komawa bakin aiki

Shugabannin kungiyyar sufuri ta birnin New-york a Amurka sun amince da komawa bakin aiki bayan kusan kwanaki uku da suka shafe suna yajin aiki.

Cimma wannan mataki dai ya biyo bayan wata tattaunawa ce da aka gudanar a tsakanin shugabannin kungiyyar sufurin da kuma wakilan mahukuntan birnin.

Dukkannin bangarorin biyu dai sun yarda daci gaba da tattaunawa akan korafe korafen da ma´aikatan sufurin suka yi a nan gaba.

Bukatun ma´aikatan dai sun hadar da karin albashi da kuma kudaden da ake bawa yan fansho.

Wannan yajin aikin dai ya jefa da yawa daga cikin mutanen birnin cikin hali na kaka ni kayin karancin abubuwan sufuri.

Bayanai dai sun nunar da cewa ako wace rana aka shiga ana yajin aikin, birnin na New- york na yin asarar Dalar Amurka miliyan 40