Ma′aikatan Red cross sun halaka a Afghanistan | Labarai | DW | 08.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma'aikatan Red cross sun halaka a Afghanistan

Su dai wadannan ma'aikatan agaji da ke tafe da direbobi uku da ma'aikata biyar an bude musu wuta a lokacin da motarsu ta dauko kayan abinci zuwa wani yankin al'umma da ke cikin tsanani na bukata.

Wasu da ake zargin mayakan IS ne sun halaka ma'aikatan agaji na Red Cross shida a Afghanistan a lokacin da suke aiki a Arewacin Afghanistan a ranar Laraban nan, kamar yadda jami'an suka bayyana. Wani abu da ke kara fito da irin hadari da ke tattare da aiki a kasar da yaki ya daidaita.

Wasu ma'aikatan agaji daga kungiyar ta Red Cross biyu kuma sun yi batan dabo bayan wani farmaki da aka kai musu a lardin Jowzjan. Daya cikin hari mafi muni da aka kai ga kungiyar agajin ta kasa da kasa a 'yan shekarun nan.

Su dai wadannan ma'aikatan agaji da ke tafe da direbobi uku da ma'aikata biyar an bude musu wuta a lokacin da motarsu ta dauko kayan abinci zuwa wani yankin al'umma da ke cikin tsanani na bukata bayan da suka fuskanci zubar dusar kankara.