Ma´aikatan jiyya na Bulgariya sun isa gida inda aka yi musu afuwa | Labarai | DW | 24.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ma´aikatan jiyya na Bulgariya sun isa gida inda aka yi musu afuwa

Ma´aikatan lafiya 6 da aka yanke musu hukuncin kisa a Libya saboda laifin sanyawa kananan yara 400 kwayoyin HIV da gangan, sun isa Bulgariya inda nan take shugaban kasar yayi musu afuwa. An koma da su gida ne sakamakon tattaunawar da aka yi jiya tsakanin jami´an Libya da kwamishinar kula da hauldodin ketare ta KTT Benita Ferrero-Waldner da kuma uwargidan shugaban faransa Cecilia Sarkozy. Shugaban Bulgariya Georgi Parvanov ya nuna farin cikinsa ga isar mutanen da suka hada da nas-nas 5 na Bulgaria da kuma likita daya Bafalasdine.