1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ma'aikatan agajin da aka kashe a Afghanistan

Mawallafi : Saleh Umar SalehAugust 9, 2010

Ƙungiyar agaji ta Christian Charity ta yi watsi da zargin cewar ma'aikan ta na yaɗa kiristanci ne a Afghanistan

https://p.dw.com/p/OgP6
Dr. Karen Woo - ɗaya daga likitocin da aka kasheHoto: AP

Wata ƙungiyar agaji ta fitar da jerin sunayen 'yan ƙetare takawas da 'yan bindiga daɗi suka kaiwa farmaki a arewacin ƙasar Afghanistan cikin makon jiya. Ƙungiyar bayar da agaji ta ƙasa da ƙasa - ta Christian Charity International ta tabbatar da cewar ma'aikatan agajin da suka gamu da ajalin su, sun haɗa da Bajamushe guda ɗaya, da ɗan ƙasar Birtaniya guda, kana da Amirkawa shidda.

A ranar jumma'ar da ta gabata ce jami'an 'yan Sanda a yankin da lamarin ya faru suka gano gawarwakin ma'aikatan waɗanda albarusai suka yi raga-raga da su. Ƙungiyar Taliban dai ta ɗauki alhakin kai harin bisa dalilin cewar, ma'aikatan agajin na yaɗa addinin kirista ne.

Sai dai darektan ƙungiyar agajin, Dirk Frans ya ce binciken su ya gano saɓanin hakan:

" Mun yi muhimman tambayoyi ga ɗaya daga cikin 'yan Afghanistan da suka tsira daga harin kuma ya shaida mana cewar sam-sam bai ga littattafan Bible ko kuma takardun adabi ba a tare da su."