Ma'aikata a bakin aiki
Ma'aikatan DW suna aiki dare da rana domin gabatar maku da labarai, rahotanni da karin bayanai da hirarraki da tara bayanai na Rediyo da Telbijin da Internet.
"Kuna sauraron Deutsche Welle..."
.......misali cikin harshen Amharic tare da mai gabatarwa Lidet Abebe dake gabatar da shirye-shirye daga tashar watsa shirye-shirye a Bonn. Amharic na daya daga cikin harsuna 30 da Deutsche Welle take gabatarwa masu sauraro a ko ina cikin duniya labarai da rahotanni ga masu sauraro da masu kallo da masu amfani da Internet.
"Babu abin da ke zama 'yar kullum......"
.....a Deutsche Welle. Wadanne labarai ne masu muhimmanci yau? Da wane wakilin DW ne mai gabatarwa zai iya yin hira da shi kai tsaye? Wadanne kanun labarai ne za mu bude shafinmu na Internet? Ga harsuna da dama, kamar na Rashanci, ko wane lokaci labarai sukan kasance da dumi-duminsu, saboda idan yamma ta yi a Bonn da Berlin, lokaci ne na fitowarrnu a Vladivostock.
"Marubuci Liao Yiwu yana amsa tambayoyi....."
.......daga Matthias Heinen, shugaban sashen harshen China. Deutsche Welle tana baiwa mutane masu yawa damar fadin albarkacin bakinsu, musamman wadanda a kasashensu ba su da 'yancin baiyana ra'ayoyinsu. Gabatar da ra'ayoyin da suka banbanta da juna abu ne mai muhimmanci a shirye-shiryen DW ga al'ummomin da ake takaita masu 'yancin samun labarai da rahotanni na hakika a kasashensu.
"Idan hirar ta yi tsawo......"
......ko kuma shin zai fi dacewa ne a yi amfani da bangaren da yafi muhimmanci cikin rahoto daga wannan hira? Daga nan edita Kishwar Mustafa daga sashen harshen Urdu zai dauki inda ake bukata ta amfani da na'urar digital ta zamani domin sauraro. Ta hakan ana iya yanka rahotanni dabam dabam domin gabatarwa masu sauraro a dakunan watsa shirye-shirye.
"Ilmantarwa ta hanyar sauraro......."
........ta hanyar wasannin kwaikwayo a shirin "Ji Ka Karu", a harsuna shida na Afirka da harsuna shida na Asiya. Wadannan wasannin kwaikwayo na rediyo misali, sukan yi bayanin yadda matasa za su bi hanyar samun sana'oi ko yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da cutar AIDS. Labaran dai marubuta matasa ne daga Afirka suke tsarawa, masu wasan kwaikwayo kuma su gabatar da su misali a Pakistan.
"Babu dai wani lokacin sararawa......"
........ga Pia Castro da abokan aikinsu, saboda sashen Telbijin na Spaniyanci yana watsa shirye-shiryen da suka kai sa'o'i 20 a kullum zuwa yankin Latinamirka. Gaba daya Deutsche Welle tana watsa shirye-shiryen Telbijin a tashoshi shida cikin harsunan Jamusanci, Ingilishi, Spaniyanci da kuma Larabci.
"Don matasa, shirin siyasa mai samun nasara......."
........wannan dai shi ne shirin mako-mako mai suna "Hirar Shabab". Wannan shiri na Telbijin yana samun masu sauraro da yawa a kasashen Larabawa. Mai gabatarwa Jaafar Abdul Karim yakan tattauna da bakinsa kan dukkanin al'amura dake daukar hankalin matasa a kasashen Larabawa - kamar "juyin juya halin Larabawa" ko kuma rayuwar baki a Jamus.
"Nahiyar Turai takan kasance kan gaba.....".
.......idan Özlem Coskun ta fara gabatar da shirinta mai suna "DW ile Avrupa", wato Turai tare da DW, wanda shiri ne mai tsawon mintoci 26. Tun daga tsakiyar 2012 wannan shirin ana iya ganin sa a tashar Telbijin ta hukuma mai suna "TRT Türk". Deutsche Welle tana kuma tsara irin wannan shiri don amfanin Telbijin a kasashen Poland, Rumaniya, Albaniya, Kroashiya, Mazedoniya da kuma Bulgariya.
"Dakika 30 kafin a fara shirye-shirye......"
Yadda mai gabatarwa ke samun damar natsuwa domin gabatar wa masu kallo manyan kanun labarai, editoci da injiniyoyi sukan taimaka domin ganin shirye-shiryen sun gudana babu tangarda. Mai ba da umurni yakan snyan rahotannin da suka samu, ya kuma shigar da abokin tattaunawa a shiri. Idan kuwa aka sami labari da duminsa, yakan canza tsarin tafiyar da shiri.
"Yi wa masu sauraro bayanin manufar raba shara a Jamus......."
.....dan Brazil! Ga Nadia Pontes da Rafael Olivera Göpfert wannan abu ne da suka saba yi yau da kullum. Sukan fassara rahotanni da karin bayanai da hirarraki, yadda 'yan Brazil masu amfani da Internet za su iya fadin albrkacin bakinsu kan al'amura na musamman da suka shafi Jamus. Ana iya karanta labarai da rahotanni daga Deutsche Welle ta Internet cikin harsuna 30.
"Ayarin Internet ya ratsa ta kasar Mali......."
.......mai rubuce-rubucen Blog Boukary Konate ne ya shirya haka, yadda mazauna kauyuka a kasarsa za su sami damar amfani da Internet. Ya sami lambar yabo ta BOBs ta Deutsche Welle a 2012, saboda Blog a shafinsa mai suna "Fasokan", a bangaren ilmantarwa da al'adu. Tun daga shekara ta 2004, DW takan ba da lambobin yabo na BOBs ga wadanda suka yi fice a tsara shafunan Internet a fannoni 17.
"Koyon aikin jarida mai inganci........"
A ko wace shekara DW takan horas da 'yan jarida matasa 20, kamar shi kansa Imtiaz Ahmad daga Pakistan. Wani al'amari na musamman shi ne tsarin horas da 'yan jarida matasa daga ko ina cikin duniya. Sashen horaswa na DW kuma, yakan hada kai da jami'ar Bonn/Rhein-Sieg domin samun takardar shaidar digiri na biyu a fannin ilimin aikin jarida na kasa da kasa.
"Ma'aikatan jarida daga ko ina cikin duniya......."
........suna iya samun karin ilimi da kwarewa daga shirin sashen horaswa na DW, misali a tsarin horaswa na lokacin bazara a yankin tsakiyar Asiya ga 'yan jarida a Bischkek, babban birnin jamhuriyar Kirgisiya. A can din masu halartar horaswan a tsawon makwanni 10 suna iya koyon tushen aiki da tsarin jarida.
"Jojo na neman cika burinsa......."
.....lokacin samun horo a Cologne. Masu koyon harshen Jamusanci sun mai da hankali, kamar wata matashiya 'yar Brazil. Bayan hotunan bidiyo da akan nuna mako-mako, masu kallo suna kuma iya amfani da shafin Facebook domin tuntubar 'yar wasan kwaikwayon. Shi wannan wasa mai suna "Jojo" yana da farin jini ya kuma sha samun lambobin yabo. 'Yar wasan kwaikwayo Dorothea Kriegl ita ce ta yi wasan "Jojo".
"Wace rawa kafofin yada labarai ke takawa....."
.....a matakan hana tashin rikice-rikice, da kare hakkin 'yan Adam ko a fannin ba da ilimi.Tambayoyi irin wadannan su ne kan gaba a taron muhawara ta 'yan jaridun duniya da ake kira "Global Media Forum" da Deutsche Welle kan shirya ko wace shekara a Bonn. Daga 17 zuwa19 ga watan Yunin 2013, taron wannan shekara zai mai da hankali kan "makomar bunkasar tattalin arziki da kafofin yada labarai".