MƊD ta kaɗa kuri´a akan tabbatar da kare ´yancin ´yan asali | Labarai | DW | 14.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MƊD ta kaɗa kuri´a akan tabbatar da kare ´yancin ´yan asali

Babbar mashawartar MDD ta kada kuri´ar amincewa da wani kuduri na kare ´yancin mutane miliyan 370 ´yan asalin yankuna ko kasashe. Kasashe 143 suka kada kuri´ar goyon bayan kudurin yayin kasashe 4 ciki har da Canada da Amirka da Australiya da kuma New Zealand suka yi watsi da kudurin wanda aiki da shi bai zama dole ba. suka ce ´yan asalin ka iya hawa kujerar naki don nuna adawa ga yadda gwamnati ke sarrafa albarkatun kasa. Kudurin wanda aka shafe sama da shekaru 20 ana muhawwara a kai ya ce ´yan asali na da ´yancin zabanwa kansu abin da suke so, mallakar kasa da albakatun tare da girmama hakokinsu kamar yadda yarjeniyoyin kasa da kasa suka tanada. A kashen kamar Canada da Bolivia, mutane ´yan asali na zargin cewa kamfanonin hakan albarkatun karakshin kasa na barazana ga hanyoyin rayuwar su.