1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dakarun gwamnati na barin wuta a Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 7, 2018

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa al'amura ka iya rincabe wa a Siriya bayan kwashe tsahon sa'o'i 48 sojojin gwamnati na luguden wuta a yankunan Idlib da gabashin Ghuta.

https://p.dw.com/p/2sGV1
Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da luguden wuta a yankunan Idlib da Ghuta
Dakarun gwamnatin Siriya na ci gaba da luguden wuta a yankunan Idlib da Ghuta Hoto: picture alliance/abaca/A. Al-Bushy

Hare-haren dai na kara ta'azzara ne a dai-dai lokacin da Majalisar ta Dinkin Duniya ke gudanar da bincike kan wanda ya kai hari da makamai masu guba a yankunan da ke hannun 'yan tawaye, wanda kuma ya hallaka fararen hula. Rahotanni sun nunar da cewa akalla mutane 70 ne suka hallaka a yankin da ke hannun 'yan tawayen wanda ke kusa da babban birnin kasar Siriyan Damascus cikin wannan mako da gwamnati ke kara zafafa kai hare-hare.