1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

LUGUDAN WUTA A FALLUJA.

zainab A Abubakar.November 9, 2004
https://p.dw.com/p/Bven
Fallujah cikin halin Ni yasu.
Fallujah cikin halin Ni yasu.Hoto: AP

Koda yammacin yau ma bata sake zani ba a dangane da kazamin hare da dakarun amurka ke cigaba da afkawa garin Falluja dasu.rahotanni sun tabbatar dacewa ana cigaba da dauki ba dadi tsakanin yan yakin sari ka noken Fallujan da kuma dakarun na Amurka a hannu guda.dakarun na Amurka dai na afkawa gidajen jamaa ne da sunan kasancewa mabuyan magoya bayan Abu al-Zarqawi,da suke nema a raye ko a mace,mutuminda ya zuwa yanzu babu wanda ya san inda yake,baya zargin da su Amurkawan keyi nacewa yana boye a wannan gari na Falluja.

A yanzu asibitocin yankin na cigaba da kira ga kasashen duniya dasu kawo agaji na magunguna da sauran bukatu na marasa klafiya saboda karuwan majinyata sakamakon wannan hali na kakanikayi da Fallujan ta fada ciki.

Saboda kalubalantar manyan makamai na zamani da Amurkawan ke amfani dasu wajen kai hare hare,yan yakin sari ka noken wadanda fuskokinsu ke rufe da hirami,kann buya ne a gine gine kafin su mayar da martani daga inda suke boye wa abokan adawan su Amurkawan.

Bugu da kari sun kuma dauki wasu matakai na ajiye mutanensu a dogayaen gine gine,wanda ke kawowa dakarun Amurkan cikas wajen kai kowane irin hari daga kasa,wadanda kuma ke harbo jiragen yaki dake shawagi ta sararin samaniya,dake yin kasa domin jefa boma bomai ,a yankuna da suke zargin yan ta sari ka noken da kasancewa.

Saboda tsananin afkawa juna da sukeyi,mayakan basu da lokacin cin abinci,face yan kananan abubuwan da yan uwansu kann kawo musu a filin daga,ayayinda ya zamanto tilas wa mazauna garin su cigaba da kasancewa a kulle a cikin gidajensu.

Gaskiyar wake rike da garin na falluja a halin yanzu dai Allah kadai ya sani,ayayinda Amurkawan ke ikirarin mamaye kashi 3 daga cikin 4 Fallujan kuma sun kusa isa tsakiyar garin,mayakan saro ka noken a hannu daya na cewa ,dakarun Amurka har yanzu suna wajen garin,basu ko kusa da shiga ba.

A halin da ake ciki yanzu haka dai kashi 10 zuwa 20 cikn 100 na alummar Falluja,daga cikin adadinsu dubu 300 ne ke cigaba da kasancewa a wannan gari,ayayinda mafiyawansu suka tsere da rayukansu zuwa wasu garuruwa,banda kuma daruruwan da suka rasa rayukansu.Maganar ruwan sha ko wutan lantarki kuwa,ya zamanto tarihi wa alummar Falluja,face wasu masallatai dake amfani da naurara samar da wutan lantarki watau generator,wadanda kuma ke kira ga mazauna garin dasu yaki kutsawan da Amurkawan ke kokarin yi a wannan yanki.

Wannan rikici na falluja dai ya dauki tsawon makonni yana gudana,inda kimanin dakarun Iraki dana Amurkia dubu 20 ke girke a wajen garin na,cikin shirin kutsawa ciki bayan da prime minista Iyad Alawi ya bada umurnin yin haka a jiya Litinin.

Harkoki kuwa na rayuwa sai kara tabarbarewa sukeyi,ayayinda tun a ranar lahadi ne wutan lantarki ya yanke baki daya,duk wasu cibiyoyi da suka hadar da makarantu da gidajen cinima kuwa sunzamanto wuraren jinya wadanda ke fama da raunuka daga wannan mummunana dauki ba dai.Garin na Falluja dai ya dawo tamkar filin wasan kwallo,domin bazaka kowa akan hanya ba da rana,daga karfe 6 na yamma kuwa dama tuni aka kafa dokar hana yawo.

A hannu guda kuma adangane da wannan hali da Fallujan ke ci,jammiyar yan darikar Sunni na kasar Irakin a yau sun sanar da ficewan su daga gwamnatin rikon kwarya da Amurka ke marawa baya a wannan kasa.