1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

LRA na kashe-kashen bayin Allah a Ƙasar Kongo

Ƙungiyar kare hakkin bila'adama dake Amurka ta zargi LRA da kashe fararen hula 320 a shekarar da ta gabata.

default

'Yan tawayen LRA na Uganda

Ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Right Watch dake birnin New York ta Amurka ta zargi ƙugiyar Lord Resistance Army ta ƙasar Uganda da hannu a kisan fararen hula 320 a shekarar bara. Bayan wannan kisan kuma ƙungiyar ta zargi LRA da sace wasu ƙananan Yara 250 a wasu ƙauyuka 10, a yankin Makombo dake Arewa maso gabashi Kongo. Rahoton wanda aka fitar dashi a birnin Kampala na ƙasar Uganda, yace an gudanar da wannan aika-aikan ne tsakanin ranakun 14 da 17 ga watan Decenban shekara ta 2009. Koda yake akasarin wa'yanda ƙungiyar ta LRA ta kashe maza ne, amma kuma akwai a ƙalla mata 13 da Yara 23. Kanfanin dillancin labaran faransa ya ruwaito Anneke Van Woudenberg mai binciken ƙungiyar mai lura da nahiyar Afurka na cewar wannan dai shine cin zarafi mafi muni da ake zargin ƙungiyar da aikatawa a cikin shekaru 23 data shafe tana yaƙin sunƙuru da Gwamnatin Uganda da zummar kafa daular mabiya addinin kirista zalla. Tuni dai kotun dake hukunta masu aikata laifukan yaƙi ta Majalisar Ɗinkin Duniya take neman shugaban ƙungiyar Joseph Kony tare da wasu kwamandojin sa biyu, ruwa a jallo.

Mawallafi: Babangida Jibril Edita: Halima Abbas