Louise Arbour ta soki Iran da taka yancin mata | Labarai | DW | 06.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Louise Arbour ta soki Iran da taka yancin mata

A yayin da ya rage kwanaki ƙalilan a gudanar da bikin ranar dunia, ta yaya mata, komishinar kulla da kare haƙƙoƙin jama´a ta MDD, Louise Arbour, da kiri taron manema labarai a birnin Geneva, na ƙasar Suizland.

Jami´ar, ta bayyana takaici, a game da yadda wasu ƙasashe, ke ci gaba da cin zarafin yaya mata.

Ta bada misali da Iran, inda a cewar ta, ranar lahadin da ta wuce, hukumomi su ka yi awan gaba, da mata fiye da 30, a lokacin da su ka shirya wata zanga-zangar lumana, gaban kotun musulunci ta ƙasa, domin neman belin wasu dangi su mata, guda 5, da halin ke cikin kurkuku.

Gwamnati na tsare da su tun ranar 8 ga watan Maris na sheakara da ta gabata.

Matan da a ka capke ranar lahadi sun shiga yajin ƙin cin abinci.

Komishina Arbour ta yi kira ga hukumomin Teheran su gaggauta sakin wannan mata.