1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Liyafar cin abincin karshe na Schröder da Chirac a paris

Zainab A MohammadOctober 14, 2005
https://p.dw.com/p/BvYj
Hoto: AP

Shugaban gwamnati mai barin gado Gehard Schroder na Jamus ,ya kai ziyaran ban kwana wa babban amininsa shugaba jacques Chirac na Faransa.

Shugaban na faransa dai na mai zama babban aminin takwaran nasa na jamus ,wadanda suka jima cikin hulda na zumunci,wanda bazai kasa nasaba da wannan ziyara ta musamman ba inda suka gudanar da liyafar cin abinci na karshe.

Wannan ziyara dai tazo ne gabannin taron kungiyar gamayyar turai,wanda zai gudana ranar 27 ga wannan wata.

Wannan liyafar cin abinci dai shine na karshen irinsa a tsaklanin shugaba Schroder akan wannan kujera da shugaba Chirac na faransa,shugabanni biyu da suka kulla dangantakar zumunci ta fanni aiki na tsawon shekaru 7 da suka gabata,a matsayin jagoran kasashe biyu dake zama masu fada aji a kungiyar gamayyar turai EU.

Shugaba Schroder zai sauka daga mukanin shugaban gwamnatin Jamus,ayayinda Angela Merkel daga Jammiyar adawa zata maye gurbinsa.

Chirac da Schroder dai zasu halarci taron kungiyar Eu a Hampton Court dake kusa da London,inda shugabannin kashen 25 ,zasu zartar a karo na karshe akan adawa da Jamus da Faransa sukayi kundun tsarin mulkin Eu din a baya,batu daya haifar da shakku dangane da yiwuwar hadin kann wakilan kungiyar domin aiki tare a matsayin tsintsiya madaurinki daya.

Kazalika yau ne sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleezza Rice takai dan takaitaccen ziyara a birnin Paris.A inda bayan ganawarsu da shugaba Jacques Chirac ta gargadi Iran data sake nazari dangane da tattauna shirin nucleanta,ko kuma a gurfanar da ita gaban komitin sulhun mdd.

A taron manema labarai data gudanar da takwaranta na faransa,Condoleezza Rice tace dole ne Iran ta tabbatarwa duniya cewa harkokin ta Nuclear na makamashi ne ,kuma basu da illa ko kuma barazana wa duniya.

Kakakin shugaban faransa yace,dashi da sakatariyar Amurkan sun amince dacewa ,bai halalta Iran ta mallaki makaman nuclear ba.To sai dai Chirac yayi nuni dacewa yana da muhimmanci acigaba da tattaunawa da kasashen jamus da britania da faransa suka fara ,tare da kulawan Rasha,wanda kuma ke bayyane wa Amurka,da bukatar Iran ta darajawa yarjejeniyar Paris da aka cimma a watan Nuwamban shekarar data gabata.

Akarkashi wannan yarjejeniya daiu Iran ta amince da dakatar da dukkan harkokinta na sarrafa sinadran uranium,wadanda Amurka da kasashen turai sukayi imanin cewa zata sarrafa makaman nuclear dasu.

A ranar 24 ga watan daya gabata nedai jamian gudanarwa na hukumar kula da yaduwar nuclear IAEA,suka cimma kuduri akan Tehran ,to sai dai amsa gabatar da ita gaban komitin sulhun ba,koda yake sun dauki matakin yin hakan.Tuun daga wannan lokaci Iran ta amince da komawa teburin tattaunawa,tare da jaddada matsayinta kann sarrfa uranium domin harkokin makamashi.