1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Live 8

July 4, 2005

A karshen mako an gudanar da kasaitaccen bikin kida na neman taimako ga kasashen Afurka, karkashin taken Live 8

https://p.dw.com/p/Bvax
'Yan kallo da suka halarci bikin kida na Live 8
'Yan kallo da suka halarci bikin kida na Live 8Hoto: AP

Alkaluma sun nuna cewar a baya ga mutane miliyan biyu da suka halarci dandalin bikin kidan da aka gudanar karkashin taken Live 8 a Hyde Park dake birnin London, an samu mutane sama da miliyan dubu biyu da suka shaidar da bikin ta gidajen telebijin a sassa dabam-dabam na duniya. Kazalika mutane sama da miliyan 25 suka gabatar da muryoyinsu ko kuma suka mika sakonni ta yanar gizo domin nuna goyan bayansu ga kiran da za a gabatarwa da shuagabannin kasashen gamayyar G8 dake fara taron kolinsu a Edinburgh a jibi laraba idan Allah Ya kai mu. Domin kuwa bisa sabanin yadda lamarin ya kasance shekaru 20 da suka wuce inda aka shirya irin wannan kasaitaccen biki domin tara kudaden taimako ga kasashen Afurka a kokarinsu na yaki da yaduwar cutar Aids, manufar bikin kidan a wannan karon shi ne matsin kaimi akan shugabannin kasashen na G8 domin su nakalci al’amuran Afurka da idanun Rahama a lokacin taron kolin nasu a Scottland. Dalilin ba wa bikin taken Live 8 shi ne domin bayyana cewar kungiyoyin makada kimanin 150 ke halartar bikin tare da ‚yan kallo miliyan biyu a baya ga wadanda zasu nakalta ta gidan telebijin su kimanin miliyan dubu 3 a sassa daban-daban na duniya domin mika sakonsu ga shuagabanni takwas da zasu gudanar da taronsu a ranar shida ga watan yuli. Ga dai abin da shi kansa mai alhakin shirya bikin Bob Geldof yake cewa:

A mayar da talauci ya zama wani lamari na tarihi, wannan shi ne ainifin manufar wannan biki. Duk kowa da kowa ya cira muryarsa domin adawa da talauci. Ba ma bukatar kudi, sai dai ku kanku. Wannan shi ne sibgar bikin a Amurka da kuma nan nahiyar Turai.

Manufofi uku masu alhakin shirya bikin suka sa gaba. Da farko yafe wa Afurka dukkan basussukan dake kanta. Sannan na biyu ribanya yawan kudaden taimakon raya kasa. Kana na uku kuma shi ne a kawar da shingen cinikin dake kassara tattalin arzikin kasashen Afurka. Wadannan manufofi kuwa kusan daya suke da wadanda ministan kudi na kasar Birtaniya Gordon Brown ke da niyyar gabatarwa a zauren taron kolin na kasashen G8, inda yake cewar:

A yafe wa kasashen Afurka basussukansu dari-bisa-dari, sannan a ribanya yawan kudaden taimako nan da shekara ta 2010 tare da kamanta adalci a harkokin ciniki.

Kusan dukkan shahararrun makada na zamani wadanda suka yi tashe a cikin shekaru 30 da suka wuce sun shiga aka dama da su a bikin na kida, wanda ya samu cikakken goyan baya daga Nelson Mandela da Bill Gates da Brad Pritt da kuma sakatare janar na MDD Kofi Annan.