1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lionel Messi na shan yabo bayan lashe kofin duniya

Mouhamadou Awal Balarabe
December 19, 2022

'Yan Ajentina na nuna farin ciki dangane da kofin duniya na uku da kasarsu ta lashe. Su ma 'yan wasanni na mika wa Lionel Messi sakon taya muna, ciki har da dan kwallon kwando LeBron James da dan wasan tennis Federer.

https://p.dw.com/p/4L9jm
Dubun dubatan mazauna Buenos Aires sun nuna farin cikin lashe kofin duniyaHoto: Diego Radames/AA/picture alliance

Daga karshe dai Lionel Messi ya ci kofin duniya na kwallon kafa, shekaru 17 bayan fara wasa a babbar tawagar kasar Ajentina. Amma sai da aka kai matakin bugun daga kai sai mai tsaron gida ne hakarsa ta cimma ruwa bayan da 'yan wasan Faransa biyu suka baras da damar da suka samu. Hasali ma dai wannan wasan karshe da ya gudana a birnin Doha yai shiga tarihi a fagen kwallon kafa, saboda tsawon mintuna 78, Ajentina ta mamaye shi tare da zura kwallaye biyu, amma dodon raga Kylian Mbappé ya rama wa kura aniyarta a cikin mintuna biyu kacal, lamarin da ya sa aka zo karshe lokacin kowa na da ci 2-2.

Karin lokaci na extra time ma bai sa a banbance dan duma da kabewa ba tun da bayan da Lionel Messi na Ajentina ya sake girgiza ragar abokan hamayyar a minti na 108, daga bisani Kylian Mbappé ya sake daukar wa Faransa fansa a bugun daga kai sai mai tsaron gida da ta ci gajiya. Sai dai ta faru ta kare wa Faransa a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da Kingsley Coman da Aurélien Tchouameni suka baras da bugun fenariti, lamarin da ya sa Faransa kasa cika burinta na zama kasa ta biyu a duniya da ta taba lashe kofin duniya sau biyu a jere baya ga Brazil.

Wannan shi ne karo na uku da Ajentina ta ci kofin duniya

FIFA Fußball WM 2022 in Katar | Finale Argentinien - Frankreich
'Yan wasan Ajentina sun yi murnar daga kofin duniya na kwallon kafaHoto: Nick Potts/PA Images/IMAGO

Wannan nasarar ta Ajentina ta zama tabarruki ga Lionel Messi, wanda ya dade yana jiran wannan kofi bayan da lashe duk lambobi da bajintocin kwallon kafa a duniya, lamarin da ya dadada magoya bayan shi da suka halarci wasa. Daya daga cikinsu ya ce: "Messi  ne gwani a cikin gwanaye. Mbappé ya taka rawar gani sosai amma Messi ne ya fi kowa taka leda, haka kuma Martinez, shi ma mai tsaron gida ya yi ban mamaki.

A bangaren Faransa kuwa, rashin nasara ya yi wa magoya baya daci, saboda kamar yadda ya faru a 2006, kungiyar kwallon kafar kasa ta yi rashin nasara a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Amma a wannan karon, bayan karon batta da Ajentina, bakin cikin bai taka kara ya karya ba. Wannan mai goyon bayan Faransa ya ce: "Wannan shi ne wasan karshe mafi kyau da aka taba yi. Mun yi rashin nasara. Wannan shi ne karo na biyu da muka yi rashin nasara a bugun fenariti tun 2006. An jijjiga mu, amma bayan rabin lokaci, ba mu yi tsammanin za mu yi nisa a wannan wasa ba. Mun yi bakin cikin rashin nasara, amma sun cancanci yabo."

Wasu kasashe sun jaya wa Faransa baya duk da bajintar Mbappé 

FIFA Fußball WM 2022 in Katar | Finale Argentinien - Frankreich
Manyan dawa na kwallon kafa a duniya: Lionel Messi da kylian MbappéHoto: Robert Michael/dpa/picture alliance

A wasu kasashen Afirka da Faransa ta raina, ma'abota kwallon kafa sun siyasantar da wasan karshe da ta yi da Ajentina sakamakon tsamin dangantakar da ke tsakaninsu a baya-bayannan. Ko da Kamaru inda hudu daga cikin 'yan wasan Faransa ke da asali ciki har da kyliam Mbappé da Aurélien Tchouameni da sauransu, sai da suka yi korafin kwace musu 'yan wasa, lamarin da ya sa da dama daga cikin 'yan Kamaru suka fito kan titin birnin Douala don taya Ajentina ta Lionel Messi murnar doke Faransa.

A Ajentina kuwa, 'yan kasa sun kwana suna rawa suna juyi don nuna farin cikinsu sakamakon wannan kofin duniya da suke jira tun shekarar 1986. Ko da shaharurun 'yan wasannin duniya ba a barsu a baya ba wajen taya Lionel Messi munar cin kofin duniya, kama daga tsohon dan kwallon Brazil Pelé har i zuwa ga fitaccen dan wasan kwallon kwando LeBron James da dan wasan tennis na kasar Switzerland Roger Federer, da dan damben kasar Rasha Khabib Nurmagomedov. Daidai da jaridun wasanni na duniya sun nuna girmamawa ga kambun Lionel Messi na Ajentina a gasar cin kofin duniya ta 2022.

Waiwaye kan gasar da Katar ta dauki bakunci 

Die besten Momente der Fußball WM 2022 Katar
Sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya ce kasarsa ta cila alkawariHoto: Martin Rickett/empics/picture alliance

Duk da cewa Katar ta kafa tarihi na kasancewar kasar Larabawa ta farko da ta dauki bakuncin kofin duniya na kwallon kafa, amma ta zama inda wata kasar Afirka ta kafa tarihi na zuwa matakin kusa da na karshe wacce ba wata ba ce illa Maroko. Ba a samu Katar da sakaci ko gazawa wajen shirye wasanni ba, amma ta sha suka game da rashin mutunta hakkin bil Adama da rashin kare hakkin ma'aikatan da suka gudanar da gine-ginen filayen kwallo, baya ga uwa uba badakalar bayar da na goro ga manyan hukumomin Turai domin tallata a duniya da ya kunno kai.

Sarki Tameem na Katar ya bayyana a yayin bikin rufe gasar da rarraba kyaututtuka cewar kasarsa ta cika duniya alkawarinta: Ya ce: "Mun yi aiki tukuru, mu da masu tayamu, don ganin wannan gasar ta yi nasara. Ga shi kuwa an yi an kare lafiya. Mun kayatar da dubun dubatan mutane da nuna musu kyawawan al'adunmu da dabi'unmu a yayin bakuntarsu da muka yi, wasu miliyoyin kuma sun ga hakan ta akwatunan talabijin"

Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya ta gaba a 2026 za ta gudana ne daga watan Yuni zuwa Yuli 2026, kuma kasashen uku ne za su hada gwiwa wajen karbar bakunci wato Amirka da Kanada da Mexico. Amma a karon farko gasar za ta tattara kungiyoyi 48  maimakon 32 kamar yadda aka saba.