Likitocin Rasha biyu sun halaka a Aleppo | Labarai | DW | 05.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Likitocin Rasha biyu sun halaka a Aleppo

Amirka da Rasha na shirin tattauna batun ficewar illahirin 'yan tawaye daga birnin Aleppo

A kasar Siriya wasu jami'an kiwon lafiya biyu 'yan kasar Rasha da suka hada da mace daya sun halaka a yayin da wani na uku ya ji munmunan rauni a cikin wasu hare-haren roka da 'yan tawaye suka kaddamar kan wani gidan assibiti na wani kauyen da ke kusa da birnin Aleppo. 

Wannan hari ya zo ne a daidai lokacin da kasashen Rasha da Amirka ke shirin soma wata tattaunawa a wannan mako kan batun ficewar illahirin 'yan tawaye daga birnin Aleppo wanda a halin yanzu dakaran gwamnatin Siriyar suka kwace sama da kashi biyu daga cikin uku na unguwannin da ke a karakshin ikon 'yan tawayen.

 Sai dai mayakan 'yan tawayen sun yi watsi da wannan tayi na ficewa daga birnin na biyu mafi girma a kasar ta Iraki tare da  shan alwashin ci gaba da yaki har sai sun ga abin da ya ture wa buzu nadi.