Likitoci a Jamus sun shiga yajin aiki | Labarai | DW | 18.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Likitoci a Jamus sun shiga yajin aiki

Likitoci a jamus sun kaddamar da wani yajin aiki na kasa baki daya suna bukatar da a kyautata tsarin albashinsu da kuma yanayin aikinsu.

Dubban likitocine dai ake saran zasuyi cuncurundo a hedikwataer maaikatar lafiyar kasar a Berlin don gabatar da korafe korafen nasu.

Ana saran akalla rabin asibitocin kasar dubu goma zasu kasance a rufe a yau yayin zanga zangar.

Bayan korafi akan rashin kyakkyawan albashi likitocin na kuma kira da a kawar da wasu tsare tsaren gwamnati na gudanar da ayyukansu wadanda suka ce na bagaira ba dalili ne da ya kamata ace ana amfani da lokatan gudanar da su wajen kula da marassa lafiya.