LIKITAN KISA A INGILA YA YANKEWA KANSA HUKUNCI... | Siyasa | DW | 13.01.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

LIKITAN KISA A INGILA YA YANKEWA KANSA HUKUNCI...

Wani likita a Kasar Biritaniya da akayiwa lakabi da suna likitan mutuwa,a yau talata ya kashe kansa da kansa ta hanyar rataya a cikin dakin da aka kulle shi a gidan maza dake can wakefield a arewacin kasar Ingila.

Harold Shipman dan shekara 58,a lokacin yana raye ya kasance mai yiwa marasa lafiyar da suka zo gunsa neman magani allurar maganadisun da zai kaisu izuwa lahira babu shiri.

A tsawon rayuwar sa Shipman ya dauki ran mutane kusan 260 ta irin wannan hanya,wanda a watan janairun shekara ta 2000 data gabata dubun sa ta cika,domin kuwa a wannan lokacin ne wata kotu ta same shi da hannu dumu dumu na aikawa da marasa lafiya izuwa lahira ta hanyar yi musu allura.

To amma duk da samun Shipman da wannan kotu tayi da laifin yin kisa na babu gaira balle dalili,ya haifar an kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike a kai,wanda shima kwamitin ya tabbatar da laifin Shipman a watan yuli na shekara ta 2002 data gabata,wanda hakan ya haifar kotun ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Daga dai lokacin da wannan kotu ta fara sauraren kasar shipman izuwa lokacin data yanke masa wannan hukunci,Kotun ta rasa gano dalilin daya sa Mr Shipman gudanar da wannan danya danyan aiki na tsawon shekaru 25 da yayi yana aikin likita a duniya.

Bugu da kari masana na fannonin ilimi daban daban suma sun rasa gano musabbabin dalilin daya haifar Mr Shipman ya dinga tafka wannan mummunan aiki a lokacin rayuwar sa yana aikin likita.

To amma a hannu daya mutanen na tunanin cewa Mr Shipman na sha,awar ganin mutum mai rai ya mutu a gabansa,wanda a ganin su hakan na daya daga cikin abubuwan da suke burge mamacin a lokacin rayuwar tasa ta aikin likitan.

A wata sabuwa kuma,wasu rahotanni da muka samu sun nunar da cewa ,a tun lokacin da Mr Shipman ya fara aikin likita a shekara ta 1974, a can garin Todmorden dake arewacin Ingila ,an taba kama shi da laifin hulda da wasu miyagun kwayoyi,wanda hakan yasa aka tursasa shi ya bar aikin,to amma daga baya yaje ya kafa asibiti na kansa,wanda ta nan ne ya dinga daukar rayukan mutane ba tare da sanin iyalan su ba.

Bisa ire iren yawan sa hannu a kann takardar mutuwa da likitoci keyi akai akai ya haifar da zargi a kann Mr shipman, daga bangaren likitoci yan uwansa,wanda hakan yasa suka kai kara gun yan sanda don gudanar da bincike a kai.

A karshe dai dubun Mr shipman ta cika ne a bayan da yan sandan suka gudanar da wannan bincike a asibitin na Mr Shipman.

A lokacin gudanar da wannan binciken ne kuma yan sandan suka gane cewa da dama daga cikin irin mutanen da Mr shipman yake kashewa mata ne da kuma tsofaffi.

A yau talata dai Mr Shipman ya yankewa kansa hukunci ta hanyar daukar ransa da yayi ta hanyar rataya a gidan yarinwakefield dake arewa maso gabashin kasar ingila.