LIBIYA TA KAU DA SAURAN SHINGE A HANYARTA TA DAWOWA CIKIN GAMAYYAR KASA DA KASA. | Siyasa | DW | 11.08.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

LIBIYA TA KAU DA SAURAN SHINGE A HANYARTA TA DAWOWA CIKIN GAMAYYAR KASA DA KASA.

Kasar Libiya, ta cim ma yarjejeniya da lauyoyin iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko kuma wadanda suka ji rauni a harin bam din nan na gidan rawar LA BELLE a birinin Berlin, ta biyansu diyya ta kimanin dola miliyan 35. Dab da hakan ne kuma, shugaba Schröder ya ce nan ba da dadewa ba, zai kai ziyara a kasar ta Libiya.

`Yan kwana kwana cikin tarkacen gidan rawar nan LA BELLE a birnin Berlin(1986), bayan tashin wani bam da ake zargin Libiya da shirya dasa shi.

`Yan kwana kwana cikin tarkacen gidan rawar nan LA BELLE a birnin Berlin(1986), bayan tashin wani bam da ake zargin Libiya da shirya dasa shi.

A halin yanzu dai, shugaban kasar Libiya, Kanar Muammar Gaddafi, ya maido da kasarsa cikin gamayyar kasa da kasa, bayan shekaru da daman da aka shafe ana yi masa saniyar ware. A jiya ne gidauniyar da ke dauke da sunan shugaban, wato gidauniyar Gaddafi, ta amince ta biya iyalan wadanda suka rayasa rayukansu, ko kuma wadanda suka ji rauni a wani harin bam da aka kai kan gidan rawar La Belle a birnin Berlin, shekaru 18 da suka wuce, jumlar kudi na kimanin dola miliyan 35. A zahiri dai, Libiyan ta ce ta yi hakan ne, ba saboda ta amince da laifin samun hannu a wannan harin da ake zarginta da shi ba. Za ta biya wadannan kudaden ne tamkar taimakon agaji ga wadanda suka raunana ko kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin.

A lokaci daya dai kuma, gidauniyar ta Gaddafi, ta yi kira ga a biya wa `yan kasarta diyya, game da harin jiragen sama da Amirka ta kai a biranen Triploli da Bengazi, kwanaki 10 bayan tashin bam a gidan rawar na La Belle a birnin Berlin. Amirka dai, a wannan lokacin, karkashin shugabancin Ronald Reagan, ta yi niyyar hambarad da shugaba Gaddafi ne da kai wa Libiya wannan harin, amma ba ta cim ma gurinta ba. Sai dai, ban da asarar kadarori masu dimbin yawa da aka yi, mutane 41, `yan kasar Libiyan ne suka rasa rayukansu, sa’annan wasu dari 2 da 26 kuma suka ji rauni. Shi kansa shugaba Gaddafin ma, sai da ya auna arziki, ya tsallake rijiya da baya. Wata `yar renonsa, Hana, ba ta tsira daga wannan harin ba. Kazalika kuma, `ya`yansa maza guda biyu, sun ji munanan raunuka.

Amma duk da hakan dai, shugaba Gaddafi bai mika wuya ba. Ya nuna matukar dauriya a cikin shekaru goman da aka yi masa saniyar ware. Tun 1982 ne dai Amirka ta sanya masa takunkumin hana shigowa da man fetur dinsa a kasar. Daga bisani ne kuma, kasashen Turai suka yi ta matsa masa lamba, don ya mika wasu `yan kasar Libiyan guda biyu, da ake tuhumarsu da shirya dasa bam a cikin jirgin saman kamfanin Amirkan nan Pan Am, wanda ya fado a garin Lockerbie a Scottland a shekarar 1988, inda mutane dari 2 da 70 suka rasa rayukansu. Sai bayan shekaru 10 ne shugaba Gaddafi ya amince a yi wa mutanen biyu shari’a a kasar Holland.

Kusan shekara daya da ta wuce ne dai, Libiyan ta amince da biyan iyalan wadanda suka rasa rayukansu a Lockerbien diyya ta kimanin dola biliyan 2 da digo 7. Har ila yau dai, a cikin watan Janairun wannan shekarar kuma, Libiyan ta amince da biyan iyalan wadanda suka rayukansu a cikin jirgin saman nan na kamafanin UTA na Faransa, wanda ya fado cikin hamada a kasar Nijer a cikin shekarar 1989, wanda kuma aka zargi Libiyan da shirya dasa bam a cikinsa. A wannan karon ma, mutane dari da 70 ne suka rasa rayukansu. A cikin watan Disamban shekarar bara ne kuma, shugaba Gaddafin ya amince a karo na farko, da bai wa sifetocin binciken miyagun makamai na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa, izinin zuwa Libiyan don su gudanad da bincike kan kafofin nukiliya da makaman guban da kasar ke mallaka. A halin yanzu dai ana ci gaba da lalata wadannan makaman.

Masharrhanta dai na ba da dalilai daban-daban kan sake alkiblar da shugaba Gaddafi yaya yi. Gwamnatin Amirka dai ta ce, fargabar kada makomarsa ta kasance kamar ta Saddam Hussein ne, ta tilasa wa shugabga Gaddafin nuna sassauci. Amma a zahiri, ba haka lamarrin yake ba takamaimai. An dai fara shawarwari kan batun Lockerbie alal misali tun da dadewa, kafin ma rikicin Iraqi ya barke.

Daya daga cikin muhimman dalilan dai, na da jibinta ne da halin tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ta Libiya ta sami kanta a ciki. Hakan kuma ya sa `yan kasar sun fara nuna alamun hasala.

Yarjejeniyar da aka cim ma jiya a birnin Berlin dai, za ta taimaka wajen fida da Libiya daga kangin saniyar waren da ta shafe shekaru da dama tana ciki. Yanzu dai babu wani shinge kuma da zai hana karbar Libiyan cikin shirin nan na kulla huldodi tsakanin kungiyar EU da kasashen yannkin bahar Rum. Ga shi dai shugaban gwamnatin tarayyar Jamus ya ba da sanarwar zai kai ziyara a Libiyan nan ba da dadewa ba. Babu shakka, hakan dai zai sake farfado da huldar cinikayya tsakanin kasashen biyu. Mai yiwuwa kuma, don mai da martani, shugaba Gaddafi ya kawo ziyara a birnin Berlin a cikin `yan watanni masu zuwa nan gaba.

 • Kwanan wata 11.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhO
 • Kwanan wata 11.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhO