Libiya: Kotu ta sake dage shari'ar Saadi Kadhafi
July 13, 2016Talla
Daya daga cikin jami'an da ke tsaron gidan kason birnin Tripoli inda ake tsare da Saadi Kadhafi, ya sanar cewa bisa tambayar lawyoyi masu bada kariya da basu samu damar halartar zaman kotun ba, an dage wannan shari'a har ya zuwa ran biyu ga watan Octoba mai zuwa.
Shi dai Saadi Kadhafi dan shekaru 42 da haihuwa, ana zargin shi ne da hada baki wajen hallaka masu zanga-zanga a lokacin soma zanga-zangar da ta yi sanadiyyar hanbare mahaifinsa a shekara ta 2011. A ranar shida ga watan Maris ne dai na 2014, hukumomin Jamhuriyar Nijar suka mika Saadi Kadhafi ga hannun hukumomin na Libiya.