Libby ya ki amsa laifin da ake tuhumar sa da aikata | Labarai | DW | 04.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Libby ya ki amsa laifin da ake tuhumar sa da aikata

A lokacin da ya gurfana gaban kotu ta farko tsohon babban jami´in gwamnatin Amirka Lewis Libby ya ki amsa laifin da ake tuhumar sa da aikata na bayyana sunan wata jami´ar hukumar leken asiri ta CIA. Har in dai aka same shi da wannan laifi Libby ka iya fuskantar hukuncin daurin shekaru har 30 a gidan yare tare da cin shi tara ta sama da dala miliyan daya. A cikin makon jiya Libby ya ajiye aikin sa a matsayin babban mashawarcin mataimakin shugaban Amirka Dick Cheney. Ana tuhumarsa da laifin yin rantsuwa kan karya da hana shari´a ta yi aiki sannan kuma ya jefa gwamnatin Bush cikin wani rikicin siyasa.