1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Legas: Cece-kuce kan biyan haraji ga wuraren ibada

April 26, 2018

Ta na kasa ta na dabo kan batun biyan kudaden haraji ga wuraren ibada na mabiya addinan Kirista da Musulmai a jihar Legas da ke kudancin Najeriya. Batun na cigaba da haifar da muhawara kan dacewa ko akasin haka.

https://p.dw.com/p/2wkkF
Nigeria Ramadan
Hoto: Getty Images/AFP/P. U. Ekpei

Kididdiga dai ta nuna cewa akwai sama da wuraren ibada dubu goma sha uku a jihar Legas, inda a wata sabuwa gwamnatin jihar a wani babi da ta bude na kwaskwarima ga dokar da ta tabbatar da biyan haraji ga gwamnati. Tuni al'ummar jihar ta Legas suka fara tafka muhawara kan batun sanya haraji ga wuraren na ibada a Legas da ke kudancin Najeriya.

Yayin da ake cigaba da maida martani kan batun, gwamnatin ta Legas ta tsame wuraren ibada da basu da kudi sosai ko kuma ba sa samun kudade daga hannun jama'ar gari. Baya ga wannan gwamnatin kasar ta ce za janye sunayen wadanda shekarunsu suka yi nisa sai dai kuma ta ce za ta yi la'akari da wasu shugabannin addinin da ke da hannu da shuni. Tuni dai shugabannin addinai suka fara maida martani game da wannan batu.