Lebanon ta yi suka ga Majalisar Ɗinkin Duniya saboda ƙyale Isra’ila da ta yi tana tura jiragen saman yaƙinta suna shawagi a sararin samaniyan ƙasar. | Labarai | DW | 26.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lebanon ta yi suka ga Majalisar Ɗinkin Duniya saboda ƙyale Isra’ila da ta yi tana tura jiragen saman yaƙinta suna shawagi a sararin samaniyan ƙasar.

Shugaban ƙasar Lebanon Emile Lahoud ya bayyana mamakinsa ga gazawar da Majalisar Ɗinkin Duniya ke yi wajen hana jiragen saman yaƙin Isra’ila kutsawa cikin sararin samainyar ƙasarsa. Wannan halin tsokana daga Isra’ilan wato take ’yancin Lebaon ne na cin gashin kanta, inji Firamiyan. Rundunar sojin Lebanon ce ta fara ba da sanarwar kutsawar jiragen saman Isra’ilan cikin sararin samaniyan ƙasar, kafin shugaba Emile Lahoud ya yi jawabinsa.

A jiya ma sai da wasu rahotanni suka ce jiragen saman yakin Isra’ila sun buɗe wa sojojin rundunar mayaƙan ruwan Jamus da ke girke a gaɓar tekun Lebanon wuta. Amma tuni Isra’ilan ta ƙaryata wannan labarin. Da yake amsa tambayoyin maneman labarai game da wannan batun, ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung, ya ce takwaran aikinsa na Isra’ila, Amir Peretz, ya tabbatar masa cewa rahotannin ba su da wani tushe, kuma ko kaɗan wannan lamarin bai taɓa aukuwa ba.