Lebanon ta roki jamus tallafin sojoji | Labarai | DW | 04.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lebanon ta roki jamus tallafin sojoji

Prime minista Fouad Seniora na Lebanon ya sanar dacewa ana shirya wasikar da zaa aikewa mdd,a inda Lebanon din ke rokon Jamus ta tura dakarunta cikin ayarin kiyaye zaman lafiya na mdd,sakamakon cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Izraela da yan Hizbollah.Premier Lebanon din yayi wannan furuci ne ,sakamakon sanarwar Jamus a akarshen mako na na janye batun tura dakarun ta na ruwa zuwa Labanon.A ranar lahadi nedai Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ,ta sanar dacewa majalisar zartarwar kasar taki amincewa da batun tura sojojin,domin bata samu takardan neman sojojin daga gwamnatin Lebanon ba.A halinda ake ciki yanzu haka dai,Qatar ta zame kasar musulunci na farko data sanar da shiga harkokin kiyaye zaman lafiya na mdd a Lebanon.Ministan harkokin wajen Qatar Hamad al-Thani ya bayyana cewa ,kasarsa zata tura dakarun soji kimanin 300.

 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5Z
 • Kwanan wata 04.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammed
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu5Z