1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lebanon ta ce za ta murƙusad da duk wani yunƙurin da ƙungiyoyin ƙasar za su yi na take ƙa’idojin tsagaita wutar da aka cim ma.

August 20, 2006
https://p.dw.com/p/BumD

Gwamnatin ƙasar Lebanon ta lashi takobin fatattakar duk wata ƙungiyar ƙasar da za ta yunƙuri saɓa wa yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cim ma a Majalisar Ɗinkin Duniya, don kwantad da ƙurar rikicin da ya ɓarke tsakaninta da Isra’ila. Ministan tsaron ƙasar, Elias al-Murr, ya faɗa wa wani taron maneman labarai a birnin Beirut cewa, dakarun ƙasar za su sa ƙafar wando ɗaya da duk wani ɓangaren da zai take ƙa’idojin yarjejeniyar. Ya ƙara da cewa, a halin yanzu, sojojin ƙasar ne ke kula da yankunan iyakarta da Siriya, kuma za su hana duk wata jigilar makamai a gun gaba ɗaya.

Jawabin ministan dai ya zo ne kwana ɗaya, bayan da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kakkausar suka da kuma zargin Isra’ila da take yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cim ma, sakamamon harin da wani rukunin sojojin ƙundumbalanta ya kai a kwarin Bekaa. Ita dai Isra’ilan ta dage kan cewar ba ta saɓa wa yarjejeniyar ba, saboda a nata ra’ayin, ta kai harin ne don hana ƙungiyar Hizbullahi yin jigilar makaman da take samu daga Siriya da Iran zuwa Lebanon don kai mata hare-hare daga nan.