Le Pen ta kaddamar da takarar shugabancin Faransa | Labarai | DW | 05.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Le Pen ta kaddamar da takarar shugabancin Faransa

Magoya bayan na Marine Le Pen sun yi ta tururuwa zuwa babbar cibiyar taron jam'iyyarsu a birnin Lyon a Faransa a wannan rana ta Lahadi da ke zama rana ta biyu ta taron jam'iyyar ta National Front.

'Yar takarar shugabancin Faransa karkashin jam'iyyar masu adawa da baki a Faransa Marine Le Pen ta bayyana cewa matakin da Birtaniya ta dauka na ficewa daga Kungiyar Tarayyar Turai da zaben Shugaba Donald Trump a matsayin shugaban Amirka wadannan dalilai ne za su sanya al'ummar Faransa su yi zabe dan samun sauyi.

Magoya bayan na Le Pen sun yi ta tururuwa zuwa babbar cibiyar taron jam'iyyarsu a birnin Lyon a Faransa a wannan rana ta Lahadi da ke zama rana ta biyu ta taron jam'iyyar ta National Front mai adawa da yawaitar baki a Faransa. Le Pen za ta yi jawabi kan abubuwa 144 da ta sanya a gaba na kokarin zama shugabar Faransa da suka hadar da batun Kungiyar EU da NATO.