1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lavrov da Kerry sun tattauna kan rikicin Siriya

Mohammad Nasiru AwalOctober 8, 2015

Rasha dai na shan suka dagane da farmakin da take kai wa IS a Siriya, amma yanzu ana kokarin hana aukuwar wani akasi da Amirka da ita ma ke kai farmaki a Siriyar.

https://p.dw.com/p/1GlIB
USA UN PK Lawrow / Kerry Treffen Nahost-Quartett in New York
Lavrov da Kerry a taron kasashen neman sulhun Gabas ta Tsakiya a New YorkHoto: picture-alliance/Zuma Press/Xinhua/Y. Bogu

Ministan harkokin wajen Rahsa Sergei Lavrov da sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry sun tattauna ta wayar tarho kan halin da ake ciki a kasar Siriya. Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bayar ta ce mutanen biyu sun yi musayar yawu kan yadda za a tuntubi juna a yakin da ake yi da kungiyar IS don hana aukuwar wani akasi musamman a sararin samaniyar kasar ta Siriya, inda jiragen yakin Rasha da Amirka ke shawagi a bama-baman da suka jefawa kan sansanonin kungiyar ta IS.