Lauyoyin Saddam Hussein sun bukaci a sallami babban alkalin da ke jan akalar shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban na Iraqi. | Labarai | DW | 01.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lauyoyin Saddam Hussein sun bukaci a sallami babban alkalin da ke jan akalar shari’ar da ake yi wa tsohon shugaban na Iraqi.

A wata sabuwa kuma, lauyoyin da ke kare tsohon shugaban Iraqi, Saddam Hussein, a shari’ar da ake yi masa da sauran mukarrabansa a birnin Bagadaza, sun yi kira ga sallamar babban alkalin kotun, kafin su amince da komawa zaman shari’ar. daya daga cikin lauyoyin Saddam din, Khalil Dulaimi ne ya bayyana haka yau a Bagadaza. A yau ne dai aka shirya sake zaman shrai’ar, bayan da matakan da alkalin ya dauka suka janyo ficewar muhimman lauyoyin wadanda ake yi musu shari’ar.

Shi dai alkalin, Rauf Rasheed Abdel Rahman, ya ki nuna wani sassauci a kotun a farkon zaman shari’ar da ya jagoranci a ran lahadin da ta wuce, abin da ya janyo ficewar Saddam Hussein daga shari’ar. Lauyoyin da ke kare wadanda ake yi musu shari’ar dai sun buga wasu sharudda 11, wadanda suka ce ya kamata a cika su, kafin su kawo karshen kaurace wa zaman kotun da suke yi.