Lauran Bagbo ya kai ziyara a wasu yankuna na ƙasar Cote d´Ivoire | Labarai | DW | 08.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lauran Bagbo ya kai ziyara a wasu yankuna na ƙasar Cote d´Ivoire

Shugaban ƙasar Cote d´Ivoire Lauran Bagbo, ya kai ziyara aiki a wasu sassa na ƙasa.

A jawabin da yayi, shugaban yi suka da kakkausar halshe, ga masu buƙatar kiffar da shi, daga karagar mulki.

A fakaice, Lauran Bagbo, ya nuna cewar tawagogin shiga tsakanin na ƙasa da ƙasa na nuna son zuciya a ayyukan da su ke gudanarwa.

Manazarta harakokin siyara a Cote D´Ivoire ,na danganta wannnan kalamomi, da wani mataki na maida hannun agogo baya, ga yunƙurin cimma zaman lahia a wannan ƙasa, da ke fama da rikicin tawaye da na siyasa.

A nasa ɓangare jiya ne, ta kamata Praministan riƙwan ƙwarya Charles Konnan Banny, ya koma gida Abijan, bayan ziyara aiki da ya kai a ƙasashen turai , to saidai, a wani mataki na ba zata, a ka bayyana ɗagewar komawar, bisa dukkan alamu, a dalili da martakan tsaro.