Lauran Bagbo ya bukaci fitar dakarun shiga tsakani daga Cote d´Ivoire | Labarai | DW | 19.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lauran Bagbo ya bukaci fitar dakarun shiga tsakani daga Cote d´Ivoire

A yayin da shugabanin ƙasashen Afrika, ke shirin tantanawa a game da rikicin Cote d´Ivoire, shugaban ƙasar Lauran Bagbo, ya yi jawabi mai zafin gaske, inda ya soki MDD, da France, a game da rawar da su ka taka, tun ɓarkewar rikicin .

Kazalika, Lauran Bagbo, ya watsa ƙasa, ga komitin shiga tsakani na ƙasa da ƙasa, da ya ƙunshi wakilai daga MDD Dunia , ƙungiyar taraya Afrika, ECOWAS da ƙungiyar gamaya turai.

Shugaban Cote d´Ivoire, ya ce sam, ya na buƙatar janyewar dakarun shiga tsakani na MDD da na France su kimanin dubu 11, wanda acewar sa, ke nuna fifiko ga yan tawaye.

Lauran Bagbo, ya haramta taron da za shirya gobe a birnin New York, a game da rikicin Cote d´Ivoire, wanda a ganin sa, wani dandali ne, kawai na sabbatu marasa ma´ana.

Saidai daga karshe ya bayyana gabatar da wasu sabinshawarwari ga kungiyar taraya Afrika wanda za su bada damar wartware rikicin.

Tun watan satumber na shekara ta 2002 kasar ta rabu gida 2, bangaren kudu cikin kular gwamnatin Abidjan, sai kuma arewa a hannun yan tawayen Guillaume Soro.