1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lardin Kosovo ba zai rabu gida biyu ba

Bayan shawarwarin da suka yi baya-bayan nan, bangarorin 3 da ake yiwa lakabi da Troika wadanda ke tattaunawa dangane da makomar lardin Kosovo sun ce lardin ba zai rabu gida biyu ba zuwa yankin Albaniyawa da Sabiyawa ba. A shirye bangarorin da suka hada da wakilan KTT da Amirka da kuma Rasha su ke, su aiwatar da kowace yarjejeniya da za´a cimma tsakanin Sabiya da Kosovo, inji Wolfgang Ischinger wakilin kungiyar EU a tattaunawar.

Ischinger:

“Wani jan aiki ke gaban mu, amma bayan tattaunawar da muka da farko a birnin Belgrade da wadda muka yi jiya da yau a Pristina, mun gano cewa sassan biyu sun yi maraba da mu kuma dukkan su biyu sun tabbatar mana da cewa a shirye suke su ba mu hadin kai.”