Larabawa na son a kafa kasar Falasdinawa | Labarai | DW | 29.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Larabawa na son a kafa kasar Falasdinawa

Shugabannin kasashen Larabawan dai sun zauna taron koli na kwana guda a gefen Bahar Mayit sun sake jadada bukatar ganin Falasdinawa sun samu 'yancin gashin kai.

Bayan makonni ana lalubar inda gwamnatin Shugaba Donald Trump ta sanya gabanta shugabanni na kasashen Larabawa a wannan rana ta Laraba sun sake jaddada cewa zaman kasashe biyu da ke makwabtaka da juna cikin girma da arziki shi ne mafita kan rikicin Isra'ila da yankin Falasdinawa.

Shugabannin kasashen Larabawan dai sun zauna taron koli na kwana guda a gefen Bahar Mayit inda suka sake jadada bukatar ganin Falasdinawa sun samu 'yancin gashin kai, sannan a tsaida mamayar da Isra'ila kewa yankinsu. A cewar Sarki Abdullah II na Jodan wanda ya dauki nauyin taron samar da kasar Falasdinawa shi ne ginshiki na samar da zaman lafiya tsakanin Laraawan da Isra'ila.