Lambar yabo ta Nobel ga Mohammed Yunus | Siyasa | DW | 13.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Lambar yabo ta Nobel ga Mohammed Yunus

Bana Mohammed Yunus daga kasar Bangladesh ne ya cancanci samun lambar yabo ta Nobel don neman zaman lafiya

Mohammed Yunus

Mohammed Yunus

A shekara ta 1976 ne Muhammed Yunus ya kirkiro cibiyarsa ta kudi a kasar Bangladesh tare da taimako daga sauran kafofi na kasa da kasa, sannan a shekara ta 1983 cibiyar ta zama banki a hukumance bisa manufar gabatar da kananan rance ga masu karamin karfi kuma kawo yanzu sama da mutane miliyan shida da dubu dari shida suka ci gajiyar wannan manufa. Bankin na da ma’aikata dubu goma sha takwas dake tafiyar da ayyukansu a kauyuka kimanin dubu saba’in da daya a kasar Bangladesh. A yayinda a zamanin baya mazauna kauyukan sai sun yi tafiya mai nisan gaske ko dai a kasa ko kuma a keke zuwa Dakha babban birnin kasar ta Bangladesh domin yin wayar tarfo a yanzu an kai musu wayoyin a kauyukansu, wanda babban ci gaba ne ga talakawa a yankunan karkara, in ji Muhammed Yunus, wanda ya ci gaba da bayani yana mai cewar:

O-Ton 3

“Bisa al’ada kauyuka a kasar Bangladesh suna can wasu yankuna ne a kuryar kasar kuma masu zama a wadannan kauyuka ba su da wata masaniya a game da abubuwan dake faruwa a sauran sassa na duniya, saboda zama saniyar ware da suka yi. Kai musu waya da aka yi ya taimaka suka samu sauki tafiyar da al’amuransu daidai da mazauna birane.”

Kwamitin kyautar yabo ta Nobel mai jami’an biyar ya sake yin ba zata wajen zabar Muhammed Yunus da Bankinsa na Grameen Bank domin karbar lambar yabon ta neman zaman lafiya a wannan shekara. Ga dai abin da Ole Donald Mjös shugaban kwamitin ke cewa dangane da haka:

“Ba za a taba samun sahihin zaman lafiya ba idan ya kasance mafi yawancin jama’a ba su da ikon fita daga cikin kangin talauci. Kananan rancen kudin da ake bayarwa yana taimakawa bisa manufa. Bugu da kari kuma ci gaban tattalin arziki shi ne babban madogarar mulkin demokradiyya da girmama ‘yancin dan-Adam.”

Bisa ga ra’ayin kwamitin lambar yabo ta Nobel zaman lafiya ba kawai ya danganci kwance damarar yaki ne kadai ba, kazalika ya hada da gwagwarmayar tabbatar da demokradiyya da kamanta adalci da kare hakkin dan-Adam da kewayensa. P/M kasar Norway Jens Stoltenberg ya kara da bayani yana mai cewar:

“Bai wa farfesa Muhammed Yunus wannan lambar kansa abu ne da ya cancanci yabo, musamman ganin yadda ya bai wa talakawa, musamman mata ‘yan rabbana ka wadatamu ikon tsayawa kan kafafuwansu. Ra’ayin ba da kananan rancen kudi ya fara ne daga kasar Bangladesh ya kuma yadu zuwa sauran sassa na duniya. Yakar talauci a duniya wani bangare ne na gwagwarmayar tabbatar da zaman lafiya.”

Farfesa Muhammed Yunus dake da shekaru 66 da haifuwa ya bayyana godiya da farin cikinsa a game da wannan lamba ta yabo ta wayar tarfo da yayi daga Bangladesh, inda ya ce wannan lambar ta yabo ba kawai tana yaba wa ayyukansa ne ba, kazalika tana mai tabbatar da ra’ayinsa ne a game da taimakon kai da kai.