Lambar yabo ta Jamus ga Ibn Chambas | Siyasa | DW | 06.10.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Lambar yabo ta Jamus ga Ibn Chambas

An miƙa wa Muhammed Ibn Chambas lambar yabo ta Jamus akan manufofin Afirka

default

Muhammed Ibn Chambas

Bana lambar yabo ta Jamus akan manufofin Afirka an miƙa ta ne ga babban jami'in diplomasiyan nan na Ghana Muhammed Ibn Chambas, wanda ake yaba masa da taka muhimmiyar rawa wajen haɗin kan yammacin Afirka da fafutukar kawo canji da samar da shugabanci na gari a nahiyar Afirka baki ɗaya. Kazalika Ibn Chambas ya taka muhimmiyar rawa wajen ba wa mulkin demoƙraɗiyya wani tsayayyen fasali a ƙasar Ghana bayan kawar da tsarin siyasar jam'iyya ɗaya a ƙasar a shekara ta 1992. A sakamakon irin rawar da ya taka ne Ibn Chambas ya cancanci samun wannan lambar Yabo ta Jamus akan manufofin Afirka a matsayinsa na shugaban hukumar zartaswa ta gamayyar tattalin arziƙin yammacin Afirka ECOWAS ya zuwa farkon wannan shekara.

Ga Ibn Chambas dai wannan lamba ta yabo da Jamus ta ba shi tamkar mutunta gwagwarmayarsa ce ta siyasa inda yake cewa:

"Ina mai karɓar wannan kyautar a matsayin wata manufa ta ba da ƙwarin guiwa akan ci gaba da ayyukana na ba da gudummawa domin kyautata makomar jin daɗin rayuwar jama'a a Afirka da ƙara kyautata nagartaccen shugabanci tare da tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a nahiyar. Kazalika ta farfaɗo da ci gaban tattalin arziƙi tare da ba ni ƙwarin guiwar ci gaba da fafutukar tabbatar da haɗin kan yankunan Afirka."

A haƙiƙa kuwa wannan shi ne ainihin muhimmin abin da Muhammed Ibn Chambas ya sa gaba a rayuwarsa. A matsayinsa na shugaban hukumar zartaswa ta gamayyar tattalin arziƙin yammacin Afirka ya zuwa farkon wannan shekarar Ibn Chambas ya duƙufa wajen daidaita banbance-banbancen dake akwai tsakanin ƙasashen yammacin Afirka da ƙirƙiro wata manufa bai ɗaya ta tattalin arziƙi tsakaninsu. Hakan kuwa ba lamari ne mai sauƙi ba ganin irin gagarumin banbancin dake tsakanin ƙasashen su kimanin goma sha biyar da suka haɗa har da Nijeriya, wadda aka ƙiyasce yawan al'umarta ya kai miliyan ɗari da hamsin da ma Kodivowa, wadda matsaloli na siyasa suka gurgunta tattalin arziƙinta. Kazalika da ƙasashe irinsu Liberiya da Saliyo, waɗanda suka taɓa fama da yaƙin basasa da kuma dawwamammun ƙasashe matasa kamar Togo da Benin. Duk da waɗannan banbance-banbance Ibn Chambas ya dage akan cewar haɗin kai ne kawai zai taimaka ƙasashen su cimma maslaharsu:

"Ana daɗa fahimtar muhimmiyar rawar da ECOWAS take takawa wajen tabbatar da shugabanci na gari da kyautata tsaro da zaman lafiya. Mutane sun gani muhimmancin gamayyar ECOWAS kuma a sakamakon haka suke ba ta cikakken goyan baya saboda sikankancewar da suka yi cewar ita ce zata biya musu buƙatunsu tare da kyautata makomar rayuwarsu."

A dai halin yanzu ECOWAS na da ga cikin ƙwararan ƙungiyoyin shiyya a nahiyar Afirka bayan fama da faɗi-tashi da ta riƙa yi bayan kafuwarta a shekara ta 1975. A wajejen tsakiyar shekarun 1990 gamayyar ta fara taka rawar gani bayan da ta canza alƙiblarta. Ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da zaman lafiya a Liberiya da Saliyo:

"Ba ma kawai ECOWAS na taka muhimmiyar rawa ba ne wajen samar da zaman lafiya da tsaro. Kazalika tana da muhimmanci wajen samar da daidaituwa akan shugabanci na gari da girmama haƙƙin ɗan-Adam da ƙarfafa mulkin demoƙraɗiyya da girmama ƙa'idojin zaɓe a shiyarmu."

Bisa ga ra'ayin jami'in diplomasiyyar dai wajibi ne ƙasashen Afirka su ɗauki ƙaddararsu a hannunsu. Su nemi bakin zaren warware matsalolinsu da kansu. Kuma wannan shi ne manufar da ECOWAS ta sa gaba.

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Muhammed Nasiru Awal