1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

091008 Ncube Afrika-Preis

Schaeffer, Ute (DW Afrika) October 15, 2008

A ranar 17 ga watannan za a bawa ɗan jarida kuma mai kamfanin buga jaridu a Zimbabwe Tevor Ncube wata lambar yabo ta Jamus ga Afirka.

https://p.dw.com/p/FaAO
Mugabe da Tsvangirai a HarareHoto: AP

Ncube zai samu wannan kyautar ne a matsayin jarumi kuma babbar muryar Afirka wanda ya bai yi ƙasa a guiwa ba wajen bayyana ra´ayinsa duk da tursasawa daga gwamnatin Zimbabwe. Masu sauraro MNA ke marhabin da saduwa da ku a wannan lokaci.

A shekarar 1989 Trevor Ncube ya fara sana´ar aikin jarida da jaridar Finanial Gazette a Zimbabwe, wanda ya zama editanta daga 1991 zuwa 1996. A shekarar 1996 Ncube ya kafa kamfanin buga jarida ta Zimbabwe Indepandent sannan shekara guda baya ya kafa kamfanin jaridar Standard a Zimbabwe. A cikin hukuncin da suka yanke alƙalan ba da lambar yabon ta Jamus sun bayyana Ncube a matsayin wani ɗan jarida da ke fitowa fili ya bayyana ra´ayinsa ba tare da jin tsoro ba duk da matsin lamba da tashe tashen hankula da tursasawa daga gwamnatin Zimbabwe.

Wannan lambar yabo da gidauniyar haɗin guiwa ta Jamus da Afirka za ta bawa Ncube na matsayin wata jaruntaka ta musamman don ƙarfafa guiwar Trevor Ncube da sauran ´yan jarida a Zimbabwe, waɗanda ke fitowa fili suna ba da labarin ainihin mawuyacin halin da ake ciki a ƙasar a fannonin siyasa da tattalin arziki saɓanin kafofin yaɗa labaru na hukuma da ke zama wata kafar yaɗa farfagandar gwamnati.

Ga Trevor Ncube wannan shaida ce ga ƙarfin zuciyar ´yan ƙasar na nuna adawa da gwamnatin mulkin kama karya kamar yadda aka gani a lokacin zaɓuka a ƙasar. An ga wannan jaruntaka a tsakanin al´umar Zimbabwe a wannan shekara inda a zagayen farko na zaɓe a watan Maris suka kaɗawa ´yan adawa ƙuri´unsu.

„Masu kaɗa ƙuri a a Zimbabwe sun nuna jaruntaka. A zagayen farko na zaɓen su fito fili sun bayyana ra´ayinsu cewa ba sa son Robert Mugabe, canji suke so. To amma tashe tashen hankula da suka zama ruwan dare gabanin zagaye na biyu na zaɓen sun sanya tsoro da fargaba a zukatan jama´a. Hakan ya karya ƙarfin guiwar jama´a musamman dangane da siyasa.“

Ga Ncube a nan ya kamata ƙungiyoyin farar hula da kuma ´yan jarida su ba da gagarumar gundunmawa.

„Dole ne a samo hanyoyin sake nunawa ´yan Zimbabwe ma´anar demoƙuraɗiyya da dukkan abubuwan da ta ƙunsa. Dole ne ƙungiyoyin jama´a su tashi haiƙan wajen yin wannan aiki. To sai dai an taƙaita musu aiki a Zimbabwe domin ana cikin wani yanayi na rashin ´yancin watsa labarai, ƙungiyoyin ba su da ´yancin kaiwa ga talakawa ta hanyar gidajen rediyo, jaridu da gidajen telebijin domin dukkan kafofin yaɗa labarun na ƙarkashin sa idon gwamnatin Zimbabwe ne. Ƙungiyoyin jama´a za su iya yin aiki ne idan suna da ´yancin kaiwa ga jama´a.“

Trevor Ncube yanzu yana zaune ne a birnin Johannesburg inda yake yiwa jaridun Mail da Guardian na Afirka ta Kudu da kuma jaridar Independent ta Zimbabwe aiki. A rahotaninsa wannan ɗan jarida da aka haifeshi a shekarar 1962 ba ya shakkar tsage gaskiya komin ɗacinta, musamman dangane da halin siyasa a ake ciki a Zimbabwe. Yana mai ra´ayin cewa hatta ita kanta jam´iyar adawa ta MDC wadda aka ba ta muƙamin firaminista, ba ta bin dokokin demoƙuraɗiyya yadda ya kamata.

„E haƙiƙa Robert Mugabe ba ya da kyau, amma ita ma MDC ba ta yin wani abin kirkiki. Ba na ganin MDC ita kaɗai za ta iya warware matsaloli masu ɗaure kai da suka yiwa Zimbabwe katutu. Ana buƙatar yiwa hukumomin ƙasar sabon fasali kuma dole a shigar da jama´a cikin wannan aiki. A nawa gani ya kamata a shigar da shugabanni kamar masana fannin tattalin arziki wajen aiwatar da canje canjen. Ya kamata dukkansu su fara wani taron haɗin kan ƙasa inda za su tattauna don samar da wata sabuwar alƙibla ga Zimbabwe.“

Tsarin mulki kama karya na jam´iya ɗaya tilo da kuma irin mulkin fir´aunanci na Mugabe wanda duk da yarjejeniyar raba madafun iko da aka cimma a cikin watan Satumba amma har yanzu ya ke ci-gaba da faɗaɗa angizonshi, ya gurɓata yanayin siyasar ƙasar. Ana buƙatar yin aiki tuƙuru kafin a iya canza wannan inji Ncube.

„Mu a Zimbabwe muna cikin wata al´uma ne da aka yi fatali da mutuncin ɗan Adam. Muna kashe junanmu saboda saɓanin ra´ayi. Mun rasa dukkan abubuwan da suka tattaru suka haɗa rayuwar ɗan Adam. Wannan shi na ke kira aƙidar ZANU-PF. Yanzu muna buƙatar wani sabon shugabancin siyasa a Zimbabwe wanda zai tashi tsayin daka wajen sanya son juna da mutunta juna tsakanin ´yan Zimbabwe.“

Kafin a tsamo ƙasar daga matsalolin tattalin arziki da rikicin siyasa dole sai an gabatar da muhimman canje canje haɗe da yarjejeniyar raba madafun iko.

„Batu na biyu shi ne kundin tsarin mulki. Dole ne mu samar da wani kundin tsarin mulki na demoƙuɗiyya wanda zai tabbatar a ´yancin ɗan Adam tare da ba su muhimmanci. Muna kuma buƙatar wata jama´a wadda za ta girmama dokokin ƙasa. Dole ne mu yiwa ma´aikatu da sauran hukumomin gwamnati kwaskwarima. Domin Mugabe ya yi nasarar mai da sojoji da ´yan sanda da hukumomin leƙen asiri da kuma majalisar dokoki ƙarƙashin ikonsa. Dole ne a mayarwa ´yan Zimbabwe ikon waɗannan hukumomin. Rundunar ´yan sanda da soji da sauran hukumomin gwamnati ta jama´a ce amma ba Mugabe ba.“

Trevor Ncube ya yi kira da a aiwatar da tsauraran canje canje don katse hanzarin Mugabe wanda yayi shekara 28 akan mulki. Ya ba da misali da Afirka Ta Kudu da kuma Jamus.

„Zimbabwe ta lalace: Mu daina ƙarya da ƙaƙarin ɓoye ainihin abin da ke faruwa. Dole mu san da haka domin mu iya gano hanyoyi magance waɗannan matsaloli. Dole mu sake lale kamar yadda ya faru a Jamus bayan sake haɗewar ta. Dole mu fuskanci gaskiya kamar yadda aka yi a Afirka ta Kudu bayan kawo ƙarshen mulkin nuna wariyar launin fata.“