Lambar yabo ga mai zanen ɓatanci ga Manzon Allah | Labarai | DW | 09.09.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Lambar yabo ga mai zanen ɓatanci ga Manzon Allah

Mai zanen ɓatancin nan ga Manzon Alla ya samu lambar yabo ta kafofin yaɗa labarai

default

Merkel na miƙa wa Westergaard lambar yabo

Ɗan ƙasar Denmark da yayi zanen ɓatanci ga manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, wanda ya haddasa bore a ƙasashen Musulmin Duniya Duniya, ya karɓi kyautar girmamamawa ta yancin faɗin albarkacin baki a nan Jamus. A jiya ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta miƙa wa ɗan Denmark mai zanen wato Kurt Westergaard lambar yabo ta kafafen yaɗa labarai. Westergaard mai shekaru 75 da haifuwa a shekaru biyar da suka gabata ya zana hoton Annabi Muhammadu sanye da bam a cikin rawaninsa, abinda ya jawo zanga zanga daga musulman duniya.

Mawallafi: Abdurrahaman Hassan

Edita: Umaru Aliyu