1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lagarde da Carstens za su fafata a IMF

June 14, 2011

Ministar kuɗin Faransa Christine Lagarde da kuma shugaban babban bankin ƙasar Mexico Agustin Carstens ne, IMF ta amince su fafata da juna da nufin neman shugabancin asusun da aka kafa bayan yaƙin duniya na biyu.

https://p.dw.com/p/11ZlM
Lagarde ta Faransa da kuma Carstens na MexicoHoto: picture alliance/dpa

Asusun ba da lamuni na duniya ya sanar da sunayen mutane biyu da suka cancaci zawarcin kujerar shugabancin wannan hukuma mai alfarma. Cikin wata sanarwa da IMF ta fitar a hedkwatartar da ke ƙasar Amirka, ta ce ministar kuɗin ƙasar Faransa wato Christine Lagarde da kuma shugaban babban bankin ƙasar Mexico wato Agustin Carstens ne za su fafata da juna da nufin maye gurbin Dominique Strauss-Kahn da ya yi murabus bisa zargin fyaɗe. Sai dai asusun bai sanya sunan shugaban babban bankin Isra'ila Stanley Fisher a cikin jerin 'yan takara ba, saboda ya shigar da takardarsa a makare.

Ƙasashe da ke samun bunƙasar tattalin arziƙi a duniya na ƙorafi dangane da ƙin martaba cancanta wajen zaɓen shugaban asusun ba da lamini. Manyan jami'an da suka fito daga nahiyar Turai ne dai ke shugabancin IMf tun bayan kafa asusun bayan yaƙin duniya na biyu. Sai dai ƙasashe masu tasuwa da ke marawa ɗan takaran da ya fito daga mexico baya suke ca da sakel.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Abdullahi Tanko Bala